Erekat ya ce kudurin Amurka na yin Allah wadai da matakan da Hamas ke dauka a zirin gaza, jirkita tsagwaron gaskiya ne. Wata sanarwar da jami'in na PLO ya fitar, yayin wani taron manema labarai, ta yi tofin Allah-tsine, game da kudurin na Amurka, wanda ke kira ga MDD da ta yi tir da ayyukan Hamas. Amurkan dai ta ce Hamas na haifar da tashe tashen hankula, tare da harba makaman roka cikin yankunan Isra'ila.
Mr. Erekat ya kara da cewa, Isra'ilan ce ya kamata ta dauki alhakin dukkanin abubuwan dake faruwa a yankin, duba da yadda take ci gaba da mamayar matsugunan Falasdinu, tana kuma kafa shingaye, da hallaka fararen hula, da tsare mutane, da kuma aikata kisan kiyashi.
Daga nan sai ya yi kira ga kungiyar Hamas wadda ke iko da zirin Gaza, da ta gaggauta amincewa da yunkurin kasar Masar, na kau da baraka tsakanin abokan tafiyar ta, tare da cimma burin hadin kai da sulhu. (Saminu Hassan)