Wang Xiaolong, ya shaidawa manema labarai cewa, taron ya haifar da kara bunkasa hadin kai a fannin aiwatar da manufofin kungiyar APEC. Ya ce Sin na dora muhimmancin gaske ga manufofin taron. Kaza lika ya ce kalaman da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi, a yayin bikin bude taron, sun kunshi wasu shawararwari game da kara bude kofa ga juna, da samar da ci gaba, da cudanya tsakanin dukkanin sassa, da inganta kirkire kirkire, da bin doka da oda, da karfafa hadin gwiwar kasa da kasa, da bunkasa tattalin arzikin duniya a tsarin gudanarwa, tare da fuskantar kalubale tare.
Game da batun gudanar da cinikayya tsakanin sassa da dama kuwa, Mr. Wang ya ce mafi yawan wakilan kasashe mahalarta taron, sun nuna goyon bayan su ga hakan, yana mai fatan kungiyar cinikayya ta duniya WTO, za ta taka rawar da ta dace, domin cimma karin nasarori a wannan fanni.
Da yake amsa tambayoyi game da fa'idojin da aka samu, a fannin cimma nasarorin raya tattalin arziki da cinikayya kuwa, Mr. Wang cewa ya yi, taron ya ciri tuta, musamman a wasu muhimman fannoni guda biyar. (Saminu Hassan)