in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya bukaci a samar da wadata ga al'ummomin Asiya da tekun Pasifik yayin kwarya-kwaryar taron shugbannin APEC
2018-11-18 16:34:46 cri

Da safiyar yau Lahadi ne aka kaddamar da kwarya-kwaryar taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar APEC karo na 26 a tashar ruwa ta Moresby dake kasar Papua New Guinea. Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya haharci taron kuma ya gabatar da jawabi, inda ya yi nuni da cewa, kamata ya yi kasashen dake yankin Asiya da tekun Pasifik, su ci gaba da nacewa ga manufar cudanyar tattalin arzikin yankin domin tsara tattalin arzikin duniya ba tare da wata rufa rufa ba, haka kuma su ci gaba da gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu, ta yadda za su ciyar da hadin gwiwarsu gaba lami lafiya.

Shugaba Xi ya kara da cewa, kasar Sin za ta kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da sauran kasashe dake yankin nan na Asiya da tekun Pisifil, tare kuma da kara zuba jari domin ba da karin gudunmowa ga ci gaba da wadata a yankin.

Babban taken kwarya-kwaryar taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar APEC karo na 26 shi ne "yin amfani da damammaki bisa tushen yin hakuri da juna domin gina kyakkyatar makoma ta zamani".

A cikin jawabin da ya gabatar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nuna ra'ayinsa a fannoni hudu, na farko, nacewa ga manufar habaka cudanyar tattalin arziki a yankin domin gina tsarin tattalin arziki mai bude kofa a yankin, na biyu, nacewa ga manufar yin kirkire-kirkire domin samun sabon karfin samun ci gaba, na uku, nacewa ga manufar kyautata tsarin yin cudanya tsakanin kasashen dake yankin domin sa kaimi kan ci gaban yankin bisa tushen yin hakuri da juna, na hudu, nacewa ga manufar kara zurfafa huldar abota domin dakile kalubale tare a yankin.

Xi ya yi nuni da cewa, duk da cewa, akwai wahala a kafa yankin cinikayya maras shinge a yankin Asiya da tekun Pasifik, amma idan sassan da abin ya shafa suka yi kokari tare, to za su cimma burin nan, misali a nace ga manufar bude kofa da yin hakuri da juna tare kuma da ingiza daidaito tsakanin juna, sai dai za a kiyaye tsarin gudanar da cinikayya dake tsakanin bangarori daban daban, tare kuma da yin adawa da ra'ayin ba da kariya ga cinikayya.

A halin yanzu, kungiyar kula da harkokin ciniki ta duniya na kokarin gudanar da sabon zagaye na gyaran fuska domin kara taka rawarta wajen kiyaye ka'idojin tsarin cinikiyya tsakanin bangarori daban daban, a don haka ya dace kasashen duniya su yi kokari tare domin ciyar da tattalin arzikin duniya gaba yadda ya kamata.

Xi ya bayyana cewa, yin cudanya abu mafi muhimamnci ne ga sassa daban daban yayin da suke kokarin cimma burin samun wadata tare, bisa tushen yin hakuri da juna, shi ya sa ya kamata a dauki matakan da suka dace domin samun ci gaba mai dorewa karkashin jagorancin muradun samun ci gaba na shekarar 2030.

Xi ya ci gaba da cewa, yanayin da kasashen yankin Asiya da tekun Pasifik ke ciki ya sha bamban, haka kuma ya kasance sabanin dake tsakaninsu, idan suna son su samu ci gaba tare, to ya kamata su martaba hanyoyin ci gaban da suka zaba, su yi musayar ra'ayoyi bisa tushen hakuri da juna ba tare da wata rufa rufa ba, da haka za su gudanar da hadin gwiwa mai moriyar juna a tsakaninsu, a karshe dai za su gina kyakkyawar makomar al'ummomin yankin Asiya da tekun Pasifik kamar yadda ake fata.

Kana shugaba Xi ya yi bayani kan matakan da gwamnatin kasarsa ta dauka, haka kuma ya yi bayani kan yadda kasar Sin take kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da sauran kasashen yankin, inda ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da gudanar da gyaran fuska a gida daga dukkan fannoni, kuma za ta kara kyautata tsarin tattalin arzikin kasuwar gurguzu tare kuma da kafa tsarin tattalin arziki na zamani, a sa'i daya kuma, kasar Sin za ta kara bude kofarta ga kasa da kasa, kuma za ta dauki karin matakan kiyaye ikon mallakar fasaha domin samar da muhallin kasuwanci da zuba jari mai inganci ga 'yan kasuwa na fadin duniya. kafin sati guda da ta gabata, kasar Sin ta shirya bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar daga ketare wato CIIE a birnin Shanghai cikin nasara, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin tana da niyyar gudanar da cinikiyya maras shinge tare kuma da bude kasuwarta ga sauran kasashen duniya, ban da haka, kasar Sin tana son kara yin hadin kai da sauran kasashen yankin Asiya da tekun Pasifik domin sa kaimi kan ci gaban tattalin arziki a yankin.

Yayin taron kolin masana'antu da kasuwancin kungiyar APEC da aka gudana jiya, shugaba Xi ya sanar da cewa, kasarsa za ta karbi bakuncin taron dandalin kolin kasa da kasa wadanda suka shiga shawarar ziri daya da hanya daya karo na biyu a watan Aflilun shekara mai zuwa. Daga baya a cikin jawabinsa yayin kwarya-kwaryar taron shugabannin APEC na yau, Xi ya bayyana cewa, yanzu shawarar ziri daya da hanya ta shiga sabon mataki na samun ci gaba, kana kasar Sin tana son samar da karin damammaki ga al'ummomin kasashen duniya baki daya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China