in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin Ta Nuna Hanyar Samun Ci Gaba Ga Kasashen Asiya Da Tekun Pasifik
2018-11-17 21:17:10 cri

 

"Muna kan jirgin ruwa na bai daya", da wannan jimlar dake bayyana yadda al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama yake ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya soma muhimmin jawabinsa a yayin taron kolin masana'antu da cinikayya na APEC da aka shirya a Papua New Guniea. A cikin jawabinsa mai tsawon minti kusan 40, shugaba Xi Jinping ya gabatar wa kasashe mambobin APEC ra'ayin kasar Sin wajen kama hanyar ci gaban tattalin arzikin duniya da neman hanyar da ta dace ta gudanar da harkokin duniya.

"Wannan ne jawabi mafi kyau a yau, na fahimci cewa, kamata ya yi duk kasashe su hada kai don samun nasara tare", Andy Kenamu, shugaban kamfanin PNG na Papua New Guinea ya bayyana haka ne bayan sauraren jawabin shugaba Xi Jinping. A nasa bangaren, Robert Apala, dan jaridar South Pacific Post ta kasar ya ce, "'Sanya jama'ar duk kasashen duniya su yi zama mai dadi', abun da shugaba Xi ya ambata ya burge ni sosai". Gaskiya jawabin da shugaba Xi Jinping ya yi ya bayyana muryar bai daya ta mahalarta taron, ya kuma dace da fata na bai daya na kasashe mambobin APEC, da kuma moriyar bai daya ta jama'ar yankin.

A taswirar tattalin arzikin duniya, shiyyar Asiya da tekun Pasifik ya kasance wani sashe mai karfi da makoma mai kyau wajen samun ci gaba. Yanzu GDP na kasashe mambobin APEC 21 ya kai kimanin kashi 60 cikin 100 bisa na duk duniya, jimilar cinikayyarsu ta kai kimanin kashi 47 cikin 100 bisa ta duk duniya. Irin nasarar da suka cimma na da nasaba sosai da kokarin da suke yi na cimma muradun Bogor wato Bogor Goals da aka tabbatar a taron kolin APEC a shekarar 1994 a matsayin jagora, da tsayawa kan gudanar da cinikayya cikin 'yanci, da kuma samar da sauki wajen zuba jari.

Yanzu wa'adin cimma muradun Bogor na shekara ta 2020 na zuwa, kuma ina za'a kwana game da hadin-gwiwar kasashe daban-daban a shiyyar Asiya da tekun Pasifik? A halin yanzu ba fuskantar damammaki da sauye-sauyen sana'o'i ke haifarwa kadai ake yi ba, har ma da kalubale da ra'ayin bada kariya ga harkokin kasuwanci da rashin kwarewar daidaita ci gaban tattalin arziki ke haifarwa. Game da hakan, shugaba Xi Jinping ya bayyana a jawabinsa cewa, ko hadin-gwiwa za'a yi ko kuma nuna kiyayya za'a yi, ko bude kofa za'a yi ko kuma rufe ta za'a yi, ko neman samun moriyar juna za'a yi ko kuma ba wanda zai ci moriya, duk wadannan batutuwa na shafar moriyar kasashe daban-daban da makomar bil'adama.

A cikin jawabin da ya gabatar, shugaba Xi ya bayyana wasu ra'ayoyinsa dake cewa, idan wata kasa ba ta bude kofarta ga duniya ba, za ta rasa duk duniya har ma ta rasa ita kanta a karshe, kuma ya kamata kasashen duniya su tsara ka'idoji cikin hadin-gwiwa, bai kamata wata kasa ita kadai ta nuna fin karfinta ga sauran kasashe ba, ko yakin cacar baki, ko yaki shi kansa, ko kuma yakin cinikayya, dukkansu ba za'a iya samun wanda zai ci nasara a karshe ba. Shugaba Xi ya kuma yi kira ga kasashe daban-daban dake shiyyar Asiya da tekun Pasifik da su karfafa hadin-gwiwa tsakaninsu, da kara mutunta juna, da samar da alfanu ga jama'a, al'amarin da zai kafa alkibla ga ci gaban shiyyar Asiya da tekun Pasifik.

A hakika, a cikin shekaru 40 da kasar Sin ta aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, kasar ta dauki hakikanin matakan inganta bunkasuwar shiyyar Asiya da tekun Pasifik. A shekarar 2016, jimillar cinikayyar da kasar Sin ta yi da kasashe mambobin APEC ta kai kaso 62% na gaba dayan cinikayyar da ta yi da kasashen duniya, a yayin da kudin jarin da ta zuba ga kasashen ya kai kaso 72% na jarin da ta zuba wa kasashen duniya baki daya.

A sa'i daya kuma, masu masana'antu da 'yan kasuwa na shiyyar su ma sun gane wa idonsu yadda kasar Sin ta yi gyare-gyare tare da bude kofarta ga kasashen ketare, sun kuma ba da gudummawarsu tare da amfana daga ciki. A jawabin da ya gabatar, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, shawarar ziri daya da hanya daya ta samar da wani dandali na yin hadin gwiwa wanda ke bude ga kowa da kowa, kasar Sin za ta ci gaba da saukaka ka'idojin shiga kasuwarta, da kuma kara kare hakkin mallakar ilmi, tare da kara habaka shigo da kayayyaki daga kasa da kasa.

A yayin da ake kara fuskantar rashin tabbas ta fannin tattalin arziki a sanadin kariyar ciniki da kuma zartar da ra'ayi na kashin kai, tattalin arzikin duniya na ci gaba da dunkulewa baki daya. A irin halin da ake ciki, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin kasuwanci ta APEC ta kasar Papua New Guinea David Toua ya ce, jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar ya bayyana ra'ayi daya na kasa da kasa.(Masu Fassarawa: Bilkisu Xin, Murtala Zhang, Lubabatu Lei, ma'aikatan sashin Hausa na CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China