in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na taimakawa kasashe tsibiran kudancin tekun Pasifik wajen kara taka muhimmiyar rawa a duniya
2018-11-17 18:02:39 cri

Xi Jinping, shugaban kasar Sin wanda a yanzu haka ke ziyara a kasar Papua New Guinea, ya gana da shugabannin wasu kasashen dake tsibiran tekun Pasifik wadanda ke da dangantakar jakadanci da kasar Sin, jiya Jumma'a a birnin Port Moresby, inda ya yi shawarwari da su tare da wakilan gwamnatocin kasashen, don musanyar ra'ayi kan zurfafa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da wadannan kasashe tsibirai, da bayar da wasu muhimman shawarwari hudu, ciki har da kara samun fahimtar juna, da neman bunkasuwa tare, da karfafa zumunta, da kuma taimakawa juna don tabbatar da adalci, al'amarin da ya bude wani sabon babi ga ci gaban alakar Sin da kasashen dake tsibiran tekun Pasifik.

A 'yan kwanakin nan, kafofin watsa labaran kasashen yammacin duniya na maida hankali sosai kan yadda kasar Sin ke kara taka muhimmiyar rawa a yankin kudancin tekun Pasifik.

Kamfanin dillancin labarai na AP na Amurka ya ruwaito cewa, akwai alamun kasar Sin a ko'ina dake birnin Port Moresby, ciki har da hanyoyi da cibiyar taron kasa da kasa da tashoshin motar bas da makamantansu, wadanda kasar Sin ta gina. Rahoton na ganin cewa, kalaman kasar Sin sun karfafa gwiwar kasashen dake yankin kudancin tekun Pasifik na cewa, suna da sabon zabi, wato kasar Sin.

Hakikanin gaskiya, galibin kasashen dake yankin kudancin tekun Pasifik, kasashe ne wadanda suka samu 'yancin kai daga Turawa 'yan mulkin mallaka bada dadewa ba, kana tattalin arzikinsu ba ya bunkasa da kyau. Haka kuma yayin da suke samun tallafin tattalin arziki daga kasashen yammacin duniya wadanda suka taba musu mulkin mallaka, su kan fuskanci matsin lamba daga garesu a fannin siyasa.

Amma ita kasar Sin, tana samar da tallafi ga kasashen dake yankin kudancin tekun Pasifik daidai gwargwadon karfinta kuma ba tare da gindaya musu wani sharadin siyasa ba, al'amarin da ya taimaka sosai ga bunkasuwar tattalin arziki da kyautatuwar zaman rayuwar al'umma a wadannan kasashe.

Alal misali, a harabar ayyukan gona da Sin da Papua New Guinea suka kafa tare bisa shawarar "ziri daya da hanya daya", ana nuna himma da kwazo wajen noman amfanin gona da kiwon albarkatun ruwa ta hanyar da ta dace, abun da ba ma kawai kyautata zaman rayuwar mazauna wurin ya yi ba, har ma da inganta kwarewar ma'aikatan wurin wajen neman bunkasuwa bisa karfin kansu.

Irin wannan tallafin da kasar Sin ke baiwa kasashen dake yankin kudancin tekun Pasifik na tada hankalin wasu kasashen yammacin duniya, wadanda suke jin tsoron rasa tasirin da suke da shi a wadannan kasashe. Har ma akwai wasu kafofin watsa labarai da masana har ma da jami'an gwamnatocin kasashen yamma wadanda suka zargi kasar Sin, al'amarin da ya janyo matukar takaicin kasashen dake yankin kudancin tekun Pasifik, inda firaministan kasar Samoa, Tuilaepa Sailele Malielegaoi ya bayyana cewa, wadannan kalamai na kasashen yamma tamkar kalaman cin zarafi ne ga shugabannin kasashen tekun Pasifik. Shi ma a nasa bangaren, ministan dokokin kasar Tonga, Sione Fa'otusia ya bayyana cewa, zargin da aka yiwa kasar Sin na cewa tana tallafawa kasashen dake yankin kudancin tekun Pasifik, abun bakin-ciki ne kwarai da gaske.

Da kasashen yammacin duniya sun gano cewa, zargin da suka yiwa kasar Sin bai yi tasiri ba, sai suka fara kwaikwayar abun da kasar Sin take yi, wato su ma suna fadada zuba jari da bada tallafi ga yankin kudancin tekun Pasifik. Amma kasar Sin ba ta damu da wannan tallafi ko kadan ba. Tallafin da kasar Sin take baiwa kasashen kudancin tekun Pasifik na shafar bangarori daban-daban. Kamar alkawarin da shugaba Xi Jinping ya yi, na cewa, kasarsa za ta bude kofar kasuwarta ga kasashe tsibiran tekun Pasifik, da fadada zuba jari, da kara shigar da kayayyakin kasashen kasar Sin, ta yadda kasashe tsibiran za su ci gajiya daga hadin-gwiwar da suke yi da kasar Sin.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China