in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da shugabannin kasashe tsibiran tekun Pasifik
2018-11-16 21:34:02 cri

A yau Jumma'a a birnin Port Moresby, babban birnin kasar Papua New Guinea, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabannin kasashe tsibiran tekun Pasifik, wadanda suka hada da shugaban tarayyar Micronesia, Peter M. Christian, da firaministan kasar Samoa, Tuilaepa Sailele Malielegaoi, da firaministan kasar Vanuatu, Charlot Salwai da firaministan kasar TheCookIslands, Henry Puna, da firaministan kasar Tonga, Akalisi Pohiva, da ma wakilin gwamnatin kasar Fiji wanda kuma shi ne ministan tsaron kasar Inoke Kubuabola, inda suka yi musayar ra'ayoyi a kan inganta huldar da ke tsakanin kasashensu, kuma baki dayansu sun yarda da daukaka dangantakar da ke tsakaninsu.

Shugaba Xi Jinping ya kuma gabatar da jawabi, inda ya gabatar da shawarwari game da bunkasa huldar da ke tsakanin Sin da kasashen a sabon yanayin da ake ciki, tare da bude sabon babin hadin gwiwarsu. Shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata a yi amfani da zarafin da ake da shi, don tabbatar da kyakkyawar makomar huldar da ke tsakaninsu. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China