in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Koriya ta arewa ya yaba da gwajin wani makamin zamani sabon kirkira
2018-11-16 11:34:45 cri

Shugaban Koriya ta arewa Kim Jong Un, ya ziyarci cibiyar kirkiro makamai ta kasar, inda ya ganewa idonsa gwajin wani makamin zamani sabon kirkira.

Kamfanin dillancin labarai na kasar KCNA da ya ruwaito labarin, bai bayyana ainihin ranar da ya kai ziyarar ba, sai dai ya ce bayan ganin gwajin makamin, Shugaba Kim cikin farin ciki, ya bayyana shi a matsayin gagarumin aiki da masana kimiyyar tsaro da masu kirkirar makamai suka yi na inganta kwarewar kasar kan harkar tsaro, inda ya kuma yaba sosai da nasarar da aka samu ta gudanar da gwajin.

Shugaba Kim ya kara da cewa, nasarar ta nuna tushen manufar jam'iyyar kwadago ta kasar, ta mayar da hankali kan kimiyya da fasahar tsaro da kara inganta kwarewar kasar kan tsaro da kuma bunkasa kwarewar rundunar sojin al'ummar Koriya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China