in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Saudiyya ta bukaci hukuncin kisa kan mutane 5 da ake zargi da hannu cikin kisan Jamal Khashoggi
2018-11-16 11:31:48 cri

Mai gabatar da kara na gwamnatin Saudiyya, ya bukaci a yanke hukuncin kisa kan mutane 5 da ake zargin na da hannu cikin kisan dan Jaridar kasar, Jamal Khashoggi.

Cikin wata sanarwa ga kamfanin dillancin labarai na Saudiyyar, mai gabatar da karan ya ce mutane 11 cikin 21 da ake zargi ne ake tuhuma, kuma za a gurfanar da su a gaban kuliya.

Ya kuma bukaci hukuncin kisa kan mutane 5 da suka bada umarnin aikata laifin, yana mai cewa za a ci gaba da binciken sauran mutanen da ake zargi don tantance irin rawar da suka taka cikin laifin.

A cewar sanarwar, mai gabatar da karar ya aike da bukatu 2 a hukumance, ga hukumomin Turkiyya a watan da ya gabata, domin su bayar da shaidu da bayanai, cikin har da na murya da aka nada game da batun.

An kuma bukaci Turkiyya ta sa hannun kan wani mataki na hadin gwiwa na musammam kan batun, inda ya ce ana jiran amsarta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China