in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen yankin Asiya da Pasific na kokarin cimma yarjejeniyar yin ciniki cikin 'yanci mafi girma a duniya a shekara mai zuwa
2018-11-15 19:52:07 cri

A shekarar da ta gabata, shugabanni na kasashe 10, mambobin kungiyar ASEAN da kasashen Sin, da Koriya ta kudu, da Japan, da Australia, da New Zealand da kuma India, sun kira taron shugabanni karo na farko game da yarjejeniyar dangantakar abokantaka ta tattalin arziki a dukkan fannoni, ta yankin Asiya da Pasific a Manila, tare kuma da bayar da wata haddadiyar sanarwa.

Bayan shekara guda, shugabanni na kasashen 16 da yarjejeniyar ta shafa, sun kira taro karo na biyu a kasar Singapore, inda baki daya suke ganin cewa, an samu hakikanin ci gaba kan shawarwari game da yarjejeniyar RCEP, kuma yanzu an shiga matakin shawarwari na karshe, inda bangarori daban daban da batun ya shafa suke kokarin kammala shawarwari kafin shekarar 2019, wannan ya nuna cewa, ana sa ran cimma wannan yarjejeniyar cinikayya cikin 'yanci mafi girma a duniya a shekara mai zuwa.

Bisa yanayin da ake ciki na fuskantar farfadowar ra'ayin yin gaban kai na wata kasa, da nuna kyamar dunkulewar tattalin arzikin duniya, da kuma kara ba da kariya ga cinikayya, shawarwarin karshe na yarjejeniyar RCEP na da ma'ana kwarai.

Da farko, yarjejeniyar RCEP za ta samar da gajiya ga mutane kimanin biliyan 3.5 dake yankin, wadanda suka kai rabin al'umman duniya baki daya. Yarjejeniyar za a samar da wani yankin cinikayya cikin 'yanci da zai kasance mafi girma a duniya, wanda yawan kudin da za a samu daga sarrafa dukiyar kasa wato GDP a takaice na yankin, zai kai dalar Amurka Triliyan 22.5. Saboda haka, shugabanni masu shiga shawarwarin sun bayyana cewa, shawarwarin na karshe game da yarjejeniyar RCEP za su yi amfani wajen karfafa imanin bangarori daban daban wajen goyon bayan ra'ayin kasancewar bangarori da dama, da gudanar da cinikayya cikin 'yanci, kuma hakan zai sa kaimi ga ci gaban tattalin arzikin yankin, da kuma dunkulewar tattalin arzikin duniya.

Na biyu kuwa, yarjejeniyar RCEP ta bayyana niyyar kasashe masu tasowa. Wani bayani da kwalejin Brookings na kasar Amurka ya fitar, ya yi nuni da cewa, yarjejeniyar RCEP ta kasance yarjejeniyar da ta fi tattare dukkanin kudurorin da ake neman cimmawa da kasashe maso tasowa suka jagoranta, wadda kuma za ta kasance yarjejeniyar ciniki maras shinge ta farko da kasashen Sin, da Indiya, da Japan, da kuma Koriya ta kudu suka cimma, bisa dokokin kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO.

Na uku, yaryeyeniyar za ta nuna gudummawar da kasashen Asiya, da suke hada kansu za su bayar ga tattalin arzikin duniya. Yarjejeniyar RCEP tana kunshe da kasashen Sin, da Japan, wadanda suka kai matsayi na biyu da kuma na uku ta fannin ci gaban tattalin arziki, haka kuma shiyyar su shiyya ce da ke kan gaba wajen samun kuzarin ci gaban tattalin arziki a duniya. Idan kuma kasashen Asiya sun hada kansu, suka kiyaye, da kuma inganta manufar kasancewar bangarori da dama, da kuma ciniki maras shinge, lallai hakan zai sa kaimi sosai ga tattalin arzikin duniya. A game da wannan, a yayin da firaministan kasar Japan Shinzo Abe ya gana da wakilai mahalarta taron ministoci game da yarjejeniyar ta RCEP a birnin Tokyo a watan Yulin bana, ya yi kira da cewa, kamata ya yi al'ummar kasashen Asiya su hada kansu, a yayin da suke tinkarar kariyar ciniki, sabo da makomar Asiya ta dogara ne ga karuwar 'yanci da adalci cikin harkokin cinikayya.

Idan mun yi hangen nesa kan shawarwarin da za'a yi a badi, za mu iya nuna imani kan yarjejeniyar RCEP. A bangaren kasar Japan kuma, bayan da ta daddale sabuwar yarjejeniyar kulla dangantakar tattalin arziki tsakanin kasashen dake yankin tekun Pasifik ko kuma TPP11 a takaice, idan za ta iya kammala yin shawarwari kan yarjejeniyar RCEP, ko shakka babu hakan zai taimaka mata sosai wajen gudanar da shawarwarin cinikayya tare da kasar Amurka. Sai dai kuma ita kasar Sin, mai karfin tattalin arziki ce, wadda ke kokarin taimakawa ga gudanar da harkokin cinikayya cikin 'yanci, da kiyaye tsarin yin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban a duk fadin duniya, za ta kuma yi namijin kokarin nuna goyon-baya ga RCEP, don ta sauke nauyin dake wuyanta. Har wa yau kasar Indiya, za ta ci alfanu sosai idan ta shiga cikin wannan yarjejeniya ta RCEP.

A halin yanzu, kasashe daban-daban a nahiyar Asiya na nuna damuwa sosai, game da ra'ayin bada kariya ga harkokin cinikayya da Amurka ke yunkurin yayatawa a duniya, al'amarin da zai karfafa musu gwiwa wajen gudanar da shawarwari kan yarjejeniyar RCEP. Akwai yiwuwar cewa, a shekara mai kamawa wato shekara ta 2019, ba ma kawai za'a iya kammala shawarwari kan yarjejeniyar RCEP ba, har ma za'a iya fara aiwatar da ita a cikin shekarar. (Masu fassara:Bilkisu Xin Lubabatu Lei Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China