Hua ta bayyana haka ne, a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Alhamis a nan birnin Beijing, inda ta kara da cewa, yarjejeniyar ta RCEP, ta kasance yarjejeniyar cinikayya cikin 'yanci mafi girma da muhimmanci a yankin Asiya da Pasific, kuma idan aka cimma yarjejeniyar, za ta shafi kusan rabin al'ummun duniya baki daya, da kusan kashi 1 cikin 3 na yawan cinikayyar duniya.
An kira taron shugabanni game da yarjejeniyar RCEP karo na 2 a jiya Laraba a kasar Singapore, wanda ya samu halartar firaministan kasar Sin Li Keqiang. Hadaddiyar sanarwar da aka fitar a gun taron ta ce, an riga an samu hakikanin ci gaba a shawarwarin na RCEP, kuma bangarori daban daban sun bayyana niyyarsu, ta cimma yarjejeniyar a shekarar 2019. (Bilkisu)