in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan tsaron kasar Isra'ila ya yi murabus
2018-11-15 13:39:58 cri
Ministan tsaron kasar Isra'ila Avigdor Lieberman ya sanar a yayin taron manema labaru da aka gudanar a majalisar dokokin kasar a ranar 14 ga wata cewa, ya yi murabus daga mukaminsa.

Lieberman ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Isra'ila ba ta dauki matakan da suka dace wajen yaki da kungiyar Hamas ba, firaministan kasar Benjamin Netanjahu ya tsaida kudurin cimma yarjejeniyar tsaigaita bude wuta a dogon lokaci tare da kungiyar Hamas, a ganinsa wannan mataki ya shaida kaza yin yaki da ta'addanci.

Lieberman ya bayyana cewa, kasar Isra'ila ta dade tana yin amfani da lalata tsaron kasar don samun zaman lafiya na gajeren lokaci.

Netanjahu ya halarci bikin tunawa da firaministan kasar Isra'ila na farko David Ben-Gurion da aka gudanar a kudancin kasar a jiya inda ya bayyana cewa, kungiyar Hamas ta roki a tsaigaita bude wuta, sun dalilin kungiyar na yin hakan.

Netanjahu ya kara da cewa, ba zai yi wani bayani game da matakan tinkarar halin da ake ciki a zirin Gaza ba, amma zai dauki matakan da suka dace don tabbatar da tsaron al'ummar kasar Isra'ila, da duk lokacin da bukatar hakan ta taso. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China