in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Najeriya suna kokarin gudanar da hadin gwiwa kan aikin gona
2018-11-15 11:01:38 cri

Idan ana son cimma burin kawar da talauci tare kuma da samun ci gaba a nahiyar Afirka, dole a ingiza ci gaban aikin gona irin zamani, yanzu wani kamfanin kasar Sin yana koyarwa al'ummun tarayyar Najeriya, kasa mafi yawan al'umma a nahiyar fasahohin aikin gona na zamani domin kara samar da hatsi a kasar.  

A bakin madatsalar ruwa ta Kanji ta jihar Kebbi dake arewa maso yammacin tarayyar Najeriya, akwai arzikin albarkatun ruwa, da kasa, da hasken rana, kuma wurin ya dace da raya aikin gona, a farkon shekarar 2006, bisa gayyatar gwamnatin Najeriya, wani kamfanin kasar Sin wato CGCOC ya zuba jari domin gina wata cibiyar aikin gona ta gwaji ta zamani a Wara, daga nan ya fara gudanar da aikinsa na raya aikin gona a nahiyar Afirka, ya zuwa shekarar 2008, kamfanin CGCOC da kamfanin raya aikin gona da kimiyya da fasaha ta zamani na Yuan Longping, wanda ya kware a fasahar kyautata shinkafa a nan kasar Sin sun zuba jari cikin hadin gwiwa a Najeriya domin kafa wani kamfanin aikin gona na yammacin Afirka a kasar, kawo yanzu cibiyar aikin gona ta Wara ta kasance sansanin shuka shinkafa da gero masu inganci.

Mai taimakawa babban manajan kamfanin CGCOC reshen Najeriya kuma babban manajan kamfanin aikin gona na yammacin Afirka Wang Yun ya yi mana bayani cewa, kawo yanzu an gina cibiyar aikin gona ta gwaji ta zamani a Wara wadda fadinta ya kai hekta dubu daya, inda aka samar da ire-iren hatsi da takin zamani da fasahar aikin gona ga manoma wadanda suke zaune a kusa da wurin, wannan ya sa manoman za su rika gudanar da aikin da kansu, tare kuma da samun karin kudin shiga, ya ce, "Yanzu muna shuka shinkafa a cibiyar aikin gona ta gwaji ta zamani a Wara, shinkafar tana da inganci matuka saboda mun zuba jari da dama a cikin shekarun baya bayan nan, kuma mun yi nazari sosai kan ingancinta, kuma mune muke mallakar fasahar, tambarin shi ne GAWAL R1, ma'anar GAWAL sunan kamfaninmu ne, ma'anar R ita ce shinkafa a Turance, 1 yana nufin lamba ta farko, yanzu haka Najeriya tana kokarin yada ingancin shinkafar a sauran kasashe mambobin kungiyar ECOWAS wato kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, manoma suna iya samun karin hatsi idan suka shuka irin wannan shinkafa har kaso 30 bisa dari, idan aka kwatanta da sauran ire-iren shinkafar da aka saba shukawa a wurin."

Wang Xuemin dan lardin Hubei na kasar Sin, yana aiki a Najeriya har tsawon shekaru 13, a baya shi ne masanin fasahar shuka shinkafa wanda ke gudanar da aikin hadin gwiwa kan aikin gona tsakanin kasashe masu tasowa a Najeriya, yanzu shi ne mai taimakawa babban manajan kamfanin aikin gona na yammacin Afirka na kasar Sin, shi ma yana kula da aikin cibiyar aikin gona ta gwaji ta zamani ta Wara, yana mai cewa, "Bayan kokarin da muke yin a kusan shekaru sama da goma da suka gabata, mun lura cewa, tunanin mazauna wurin ya sauya, yanzu dai kamar yadda mu Sinawa muke, 'yan Najeriya su ma suna kara mai da hankali kan fasahar zamani yayin da suke gudanar da aikin gona, a don haka hatsin da suke samu ya karu matuka."

Ban da cibiyar aikin gona ta gwaji ta zamani ta Wara, kamfanin CGCOC shi ma ya kafa wata cibiyar aikin gona ta kimiyya da fasahar zamani a Abuja, fadar mulkin tarayyar Najeriya, nan gaba Sin da Najeriya za su kara gina wata cibiyar gwaji kan fasahar aikin gona cikin hadin gwiwa a cibiyar.

Bulus Inusa, wani 'dan Najeriya ne mai shekaru 34, ya taba shuka kayan lambun gida, yanzu haka yana aikin kula da fasahar shuka kayan lambu a cibiyar dake Abuja, yana ganin cewa, akwai bambanci tsakanin fasahar gargajiyar iyalinsa da fasahar zamani da ya koya a cibiyar, yana mai cewa, "Akwai wani tsarin fasaha a nan, amma a baya sai dai mu zuba iri a gona kawai, masanin kasar Sin ya koyar mana fasahohin da aikin ya shafa, misali yadda ake gyara gona, da yadda ake shuka kayan lambu, da yadda ake ban ruwa a gona da sauransu, mun karu sosai daga wajensa, yana da kirki, kullum yana taimaka mana ba tare da bata lokaci ba."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China