in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ICPC za ta binciki shugaban jam'iyyar APC bisa zargin cin hanci
2018-11-15 09:30:02 cri

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya ko ICPC a takaice ta ce za ta binciki zargin karbar na goro da ake yiwa shugaban jam'iyyar APC mai mulkin kasar Adams Oshiomhole a lokacin zaben fidda 'yan takarar jam'iyyar da aka kammala ba da dadewa ba.

Mai magana da yawun hukumar Rasheedat Okoduwa ita ce ta bayyana hakan ga manema labarai a Abuja, fadar mulkin kasar.

Shawarar da hukumar ICPC ta yanke ta bincikar shugaban na APC na zuwa ne mako guda bayan da 'yan sandan farin kaya na kasar suka tuhume shi bisa zargin yin ba dai-dai ba a zaben fidda 'yan takarar jam'iyyar, inda aka bukace shi da ya sauka daga mukaminsa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China