in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi zai halarci kwarya-kwaryar taron shugabannin APEC karo na 26
2018-11-14 11:08:18 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyarar aiki kasashen Papua New Guinea da Brunei da Philipines tsakanin ranakun 15 zuwa 21 ga wannan wata, inda zai yi ganawa da shugabannin kasashen tekun Pasifik wadanda suka kulla huldar diplomasiyya da kasarsa, kana zai halarci kwarya-kwaryar taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar APEC karo na 26.

Jami'an ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin da ma'aikatar kasuwancin kasar sun bayyana cewa, wannan ne karo na farko da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara wadannan kasashe uku, haka kuma shi ne karo na farko da zai gana da shugabannin kasashen dake tekun Pasifik wadanda suka kulla huldar diplomasiyya da kasar Sin a cikin shekaru hudu da suka gabata, ko shakka babu ziyarar tana da babbar ma'ana kan ci gaban huldar dake tsakanin kasarsa da kasashen nan uku wato Papua New Guinea da Brunei da Philipines da kuma kasashen dake tekun Pasifik wadanda suka kulla huldar diplomasiyya da kasar Sin, a sa'i daya kuma, wannan shi ne karo na shida da Xi ya halarci ko ya jagoranci kwarya-kwaryar taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar APEC, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin tana mai da hankali matuka kan hadin gwiwar tattalin arziki dake tsakaninta da kasashen dake yankin tekun Pasifik da Asiya.

Kasashen dake tekun Pasifik muhimman kasashe ne a yankin tekun Pasifik da Asiya, kana muhimman kasashe ne masu tasowa, kasashen dake tekun Pasifik wadanda suka kulla huldar diplomasiyya da kasar Sin sun hada kasashe takwas wato Papua New Guinea da Fiji da Samoa da Vanuatu da wasu hudu. A shekarar 2014, shugaba Xi ya taba ganawa da shugabannin kasashen, inda suka tsai da kudurin kafa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare bisa tushen martaba juna. A cikin shekaru hudu da suka gabata, huldar dake tsakaninsu ta samu ci gaba cikin sauri, musamman ma a fannonin cinikayya da zuba jari da tattalin arziki da fasaha da gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a da cudanyar al'adu. Ya zuwa shekarar 2017, kwatankwacin darajar cinikayyar dake tsakanin kasar Sin da kasashen nan takwas ya kai dalar Amurka biliyan 7 da miliyan 200. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zheng Zeguang ya bayyana cewa, ziyarar da Xi zai kai kasashen za ta daga matsayin huldar dake tsakanin sassan biyu, haka kuma za ta taimaka ga ci gaban hadin gwiwar dake tsakaninsu, kana za ta yi babban tasiri ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a wannan yanki na tekun Pasifik da Asiya, Zheng ya jaddada cewa, "Kasar Sin tana gudanar da hadin gwiwa tsakaninta da wadannan kasashe takwas ne karkashin jagorancin tsare-tsaren hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, misali hadin gwiwar moriyar juna da zuba jari kan kamfanoni da samar da taimako tsakanin gwamnatoci da sauransu, dole ne a bayyana cewa, kasar Sin tana samar musu taimako ba tare da gindaya wani shardi ba, lamarin ba shi da nasaba da sauran kasashe ko kadan, muna son gudanar da hadin gwiwa da sauran kasashe bisa tushen amincewar kasashen dake yankin tekun Pasifik, domin dakile matsalolin da suke fuskanta, tare kuma da cimma burin samun ci gaba mai dorewa a kasashen."

Kasar Papua New Guinea ce za ta jagoranci taro na bana, babban taken taron shi ne "Samar da damamamkin ci gaba bisa tushen hakuri da juna domin gina makoma ta zamani", bangarorin da za su halarci taron za su tattauna kan batutuwan dake shafar cudanyar tattalin arziki a yankin da tattalin arziki na zamani da cudanyar juna da samun ci gaba mai dorewa bisa hakuri da juna da sauransu, mai taimakawa ministan harkokin wajen kasar Sin Zhang Jun ya bayyana cewa, Xi zai gabatar da muhimmin jawabi yayin taron shugabannin 'yan kasuwa da masana'antu na APEC, da kuma kwarya-kwaryar taron shugabannin APEC, Zhang Jun ya yi nuni da cewa, "Muna fatan za su samu sakamako a fannoni hudu wato gina tattalin arziki ba tare da wata rufa rufa ba da sa kaimi kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashen yankin da zurfafa huldar abokantaka tsakanin kasashen da bullo da shirin hadin kai nan da shekarar 2020 domin ciyar da APEC gaba yadda ya kamata."

Kana Xi zai kai ziyarar aiki kasashe Brunei da Philipines tsakanin ranakun 18 zuwa 21 ga wata, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Kong Xuanyou ya ce, ziyarar tana da babbar ma'ana ga huldar dake tsakanin Sin da kasashen biyu, a cewarsa: "Sin da Brunei kasashe ne makwabta, bana shekaru biyar ke nan da kulla huldar diplomasiyya tsakaninsu, Philipines ita ma abokiyar kasar Sin ce, muna fatan za mu ciyar da huldar dake tsakaninmu gaba lami lafiya."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China