in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fashewar bam ta halata mutane 3 a Mali
2018-11-14 11:02:29 cri
Ma'aikatar harkokin tsaron kasar Mali ta sanar a jiya cewa, an kai wani harin bam da aka dana a cikin mota a birnin Gao dake arewacin kasar Mali a daren ranar 12 ga wata, wanda ya haddasa mutuwar mutane 3 tare da raunata wasu mutane 2.

Sanarwar ta bayyana cewa, bam din da aka dana a cikin motar ya tashi ne da karfe 8 na daren ranar 12 ga wata agogon wurin kusa da gidajen jama'a dake birnin Gao, wutar da fashewar bam ta haddasa ta lalata gidajen dake kewayen. Sanarwar ta yi kira ga jama'a da su kwantar da hankali su kuma kauracewa wurin.

Rahotannin kafofin watsa labaru na kasar Mali na cewa, kungiyar masu tsattsauran ra'ayi dake da nasaba da kungiyar al-Qaeda ta sanar da daukar alhakin kai harin.

Yankin arewacin kasar Mali ya sha fama da rikice-rikice a 'yan shekarun baya baya nan, kana an fara samun rikice-rikice da hare-haren ta'addanci a tsakiyar kasar. A sakamakon mummunan yanayin tsaro da ake fama da shi a kasar, gwamnatin kasar Mali ta gabatar da daftarin doka ga majalisar dokokin jama'ar kasar a ranar 24 ga watan Oktoba, inda ta bukaci a tsawaita wa'adin dokar-ta-bace a kasar har zuwa ranar 31 ga watan Oktoba na shekarar 2019. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China