Darektan wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a birnin London na kasar Burtaniya, ya ce, bukatar amfani da iskar gas na karuwa matuka. Yanzu haka tasirin kasar Sin a kasuwar iskar gas dai-dai yake da tasirin da aka gani shekaru 10 da suka gabata a fannin bukatar kasar ta Sin a kasuwannin mai.
Birol ya ce, kasar Sin ta zama kasar da ta fi kowace kasa shigo da iskar gas a duniya, inda ta sha gaban kasar Japan, kuma wannan yana da matukar illa ga kasuwa da ma farashin na gas.
Sai dai kuma rahotanni na cewa, bukatar gas a duniya za ta karu da kaso 1.6 cikin 100 a kowace shekara har zuwa shekarar 2040, inda bukatar za ta karu da kaso 45 cikin 100 kan bukatar da ake da ita a halin yanzu, ciki har da Iskar gas wadda ake hasashen za ta zama kafar makamashi ta biyu a duniya nan da shekarar 2030 bayan makamashin kwal, yayin da manyan masu amfani da makamashi a duniya ke kokarin rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli. (Ibrahim Yaya)