in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ina Dalilan Da Suka Sanya Sinawa Ke Sa Ran Alheri Kan Makomar Kasarsu A Nan Gaba
2018-11-13 20:08:55 cri
Bisa sabon rahoton da Economist Intelligence Unit na kasar Burtaniya ya bayar game da bincike kan jama'ar kasashe 50, an nuna cewa, Sinawa kashi 91.4% na sa ran alheri kan makomar kasarsu a nan gaba. A ganin su, kasar Sin za ta ci gaba da samun bunkasuwa a cikin shekaru 10 masu zuwa, tare da karfafar al'umma mafi kyau.

Shekarar da muke ciki, shekara ce ta cika shekaru 40 da aka aiwatar da kwaskwarima a cikin gida, da bude kofa ga kasashen ketare a nan kasar Sin, wannan ne sha'ani na kawo manyan sauye-sauye ga kasar Sin, da duk duniya baki daya, a ta bakin shugaban kasar Sin Xi Jinping. Wannan bincike da aka yi ya nuna cewa, dalilan da suka sanya yawancin Sinawa ke sa ran alheri kan makomar kasarsu, su ne wadata da nasarorin da kasar ke kawo musu, sakamakon yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare a cikin shekaru 40 da suka gabata, da kuma fatansu da amincewar da suke nunawa, kan manufar da kasarsu ke bi wajen ci gaba da gudanar da aikin a nan gaba.

A hakika, kasar Sin na ci gaba da fuskantar matsaloli da dama, a kokarinta na bunkasa zaman al'umma. Misali, shugabannin kasar Sin sun bayyana babbar matsalar da ake fuskanta a kasar a zamanin yanzu, a matsayin yadda al'umma ke kara neman biyan bukatunsu na rayuwa mai dadi, da kuma yadda ake fama da rashin samun daidaiton ci gaba a sassan kasar, har ma sun yi niyyar shafe tsawon shekaru uku wajen magance manyan matsaloli, da saukaka fatara, da kuma daidaita gurbacewar muhalli, matakin da zai sa kasar Sin ta kai ga samun ci gaba mai inganci.

A makon da ya gabata ne, a yayin da ake dab da cika shekaru 40, da kasar Sin ta aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida, da kuma bude kofa ga kasashen waje, masu sayayya na kasar Sin da kasashen duniya, suka karya matsayin bajinta da ake da shi a fannin sayayya ta yanar gizo. Wato a Lahadi, ranar 11 ga wata, ranar da a kowace shekara Alibaba, babban kamfanin cinikayya ta intanet, ya kan kaddamar da garabasar sayayyarsa tun daga shekarar 2009, kuma a ranar ta wannan shekara, yawan darajar kayayyakin da aka saya ya wuce dalar Amurka biliyan 30, abin da ya kasance yabo ne ga makomar tattalin arzikin kasar Sin. (Masu fassara: Bilkisu Xin Lubabatu Lei, dukkansu ma'aikatan sashen Hausa na CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China