Kakakin ma'aikatar lafiya ta Gaza, Ashraf al-Qedra, ya shaidawa manema labarai cewa, an gano mutane 3 da suka mutu, wadanda suka hada da Mohamed al-Tatari mai shekaru 27 da Mohamed Oudeh mai shekaru 22 da kuma Hammad al-Nahal mai shekaru 23.
Wani ganau ya ce jiragen yakin Isra'ila sun auna wani gida ne dake garin Rafa na kudancin zirin Gaza.
Wata gajeriyar sanarwa da kawacen kungiyar mayakan Falasdinu, ciki har da Hamas ta fitar, ta tabbatar da aukuwar hare-haren, inda ta ce dakarun kungiyar sun harba rokoki daga zirin Gaza zuwa matsugunan 'yan adawa da yammacin jiya Littinin. (Fa'iza Mustapha)