Rahoton wanda aka wallafa bayan gudanar da bincike kan wasu kasashen duniya 50, ya duba irin yadda al'ummun kasashen ke ji a zukatansu game da kasashen nasu.
Kazalika wani bangare na rahoton ya bayyana yadda kasashe masu tasowa irin su Sin da India, ke kara kaimi wajen bunkasa fannonin kimiyya da fasaha, musamman ma fannin kwaikwayar tunanin bil Adama, yayin da a Afirka kasashen nahiyar ke maida hankali wajen bunkasa fasahohi daga matakai na tushe, domin shawo kan karancin ababen more rayuwa.(Saminu Alhassan)