in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata kotu a Masar ta tabbatar da hukuncin kisan da aka yankewa wasu mutane 7 bisa zargin su kashe wani dan sanda
2018-11-12 14:00:59 cri

A jiya ne wata babbar kotun a kasar Masar ta tabbatar da hukuncin kisan da a baya aka yanke wa wasu mutane bakwai, bisa zargin su da laifin kashe wani dan sanda a shekarar 2013.

Kotun kula da manyan laifuka dake Isma'iliya dake arewa maso gabashin birnin Alkahira ce dai ta yanke wannan hukunci a baya, bisa zargin da ake yiwa mutanen bakwai da kashe wani dan sanda mai suna Ahmed Radwan Abu-Doma tare da kwace bindigarsa da kuma kaiwa jami'an tsaro dake sintiri hari a karshen shekarar 2013.

Hukuncin dai ya tabbata, kuma ba za a daukaka kara ba, domin babbar kotun ta yi watsi da karar da masu kare wadanda ake kara suka gabatar.

Binciken da aka gudanar a baya dai ya nuna cewa, 'yan bindigar suna kan babur ne da kuma wata mota a lokacin da suka kaiwa jami'an tsaron hari inda suka yi musayar wuta.

An kuma yankewa wasu mutane biyu da ke kare wadanda ake zargi hukuncin daurin shekaru 2 da kuma uku a gidan yari, saboda boye wadanda ake tuhuma.

Kasar Masar dai ta sha fama da ayyukan 'yan ta'addan da suka kai ga kisan 'yan sanda da sojoji da ma fararen hula, sakamakon boren da ya samu goyon bayan sojojin kasar da ya kai ga hambarar da shugaba Mohamed Morsi a farkon watan Yulin shekarar 2013.

Kungiyar 'yan ta'addan yankin Sinai dake goyon bayan IS ke ikirarin kai galibin hare-haren ta'addancin da ake kaiwa kasar ta Masar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China