in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinawa suna kara sha'awar yin sayayya a ranar gwagware
2018-11-12 11:01:40 cri

Da tsakar daren ranar 11 ga watan Nuwamba ne aka kaddamar da bikin sayayya na ranar gwagware na kasa da kasa na shekarar bana, alkaluma na nuna cewa, cinikin da shagon TMall ya yi a wannan ranar ya kai RMB yuan biliyan 213 da miliyan 500, kana cinikin da shagon JD ya yi a ranar shi ma ya kai RMB yuan biliyan 159 da miliyan 800, masanan da abin ya shafa sun bayyana cewa, karuwar cinikin da aka samu a cikin shekaru goma da suka gabata, na nuna cewa, Sinawa suna kara nuna sha'awar yin sayayya ta yanar gizo, haka kuma suna kara mai da hankali kan ingancin kayayyakin da suke saya a yau da kullum.

A ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 2009, Alibaba, babban kamfanin cinikayya ta intanet na kasar Sin ya kaddamar da ranar gwagware, kawo yanzu shekaru goma ke nan da aka fara wannan gaggarumin shiri na kasa da kasa, kuma alkaluman na nuna cewa, cinikin da kamfanin Alibaba ya yi a shekarar 2009 yuan miliyan 52 kawai, amma bana cinikin kamfanin ya kai yuna biliyan 1 a cikin dakika 21 tun bayan da aka kaddamar da shirin a tsakar daren ranar, an bayyana cewa, ko a yanar gizo, ko a cikin kasuwanni, ko a kasar Sin, ko a kasashen ketare, bikin ranar gwagware ya sa babban kuzari ga masu sayayya kamar wuta mai zafi a yanayin sanyi, lamarin da ya nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana da karfi matuka, haka kuma ya nuna cewa, masu sayayya suna cike da imani kan kasuwar kasar ta Sin.

Darektan ofishin nazarin sabon yanayin da tattalin arizki ke ciki na cibiyar nazarin manufofin raya kasa ta majalisar gudanarwar kasar Sin Zhu Min ya bayyana cewa, karuwar cinikin da aka samu a cikin shekaru goma da suka gabata, na nuna karfin sayayya na al'ummun kasar Sin ya dagu a bayyana, yana mai cewa, "An samu karuwar ciniki a cikin shekaru goma da suka gabata, haka kuma ingancin sayayyar Sinawa ya kyautata, dalilin da ya sa haka shi ne domin gwamnatin kasar Sin tana kara mai da hankali kan ingancin kayayyaki, da na rayuwar al'ummarta,."

Alkaluman da kamfanin Alibaba ya samu sun nuna cewa, masu sayayya a kasar suna kara nuna sha'awa kan kayayyakin da za su kyautata rayuwarsu a maimakon kayayyakin da suke bukata na yau da kullum, misali adadin kudin da kamfanin ya samu daga sayar da sabuwar wayar salula ta IPhone ya kai yuan miliyan 100 a cikin mintuna 30 bayan da aka kaddamar da shirin, kana an sayar da daukacin jiragen sama masu sarrafa kansu samfurin Osmo, da na'urar daukar bidiyo samfurin GoPro, da na'ura wasa mai kwakwalwa samfurin ThundeRobot a cikin awa guda daya kacal bayan da aka kaddamar da shirin.

Ban da haka, alkaluman da shagon JD ya samu sun nuna cewa, masu sayayya sun fi sha'awar kayayyakin da ake amfani da su a cikin gida, da abinci masu gina jiki, da motoci da sauran kayayyakin da suke kyautata ingancin rayuwa.

Hakazalika, kayayyaki masu inganci da hajojin da ake shigo kasar daga ketare su ma suna kara jawo hankalin masu sayayya a kai a kai, masanin cibiyar nazarin harkokin kasuwanci ta ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Zhou Mi ya bayyana cewa, a cikin wadannan shekaru goma da suka gabata, kayayyakin kasashen ketare suna kara karuwa a sakamakon dandalin sayayya ta yanar gizo da ake samarwar, yanzu masu sayayya suna da zabi a dandalin, 'yan kasuwa suna yin gogayya tsakaninsu yadda ya kamata, a don haka masu sayayya suna samun moriya daga wajen, yana mai cewa, "Dalilin da ya sa ranar gwagware ya kara jawo hankalin masu sayayya shi ne domin suna iya sayen karin kayayyakin da suke bukata a dandalin, misali a baya ana sayar da jar barasa ta kasar Faransa ne kawai a kasar Sin, amma yanzu ana iya sayen su na kasashen Chile da Afirka ta Kudu da kuma Latin Amurka, masu sayayya suna da dama zabar wadda suke so."

Zhou ya kara da cewa, alkaluman na nuna cewa, yanzu cinikayyar dake tsakanin kasar Sin da kasashe masu ci gaba tana kara karuwa, ya ce, nan gaba ya kamata a kara samar da hanyoyin ciniki a dandalin kasuwanci kan yanar gizo, domin samar da karin zabi ga masu sayayya na kasar Sin, haka kuma kamfanonin za su iya samun ci gaba, yana mai cewa, "Misali ana gudanar da cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen Amurka da Australia da sauran kasashe masu ci gaba lami lafiya, amma kasashen Afirka kalilan ne suke gudanar da cinikayya ta yanar gizo da kasar Sin, shi ya sa nan gaba ya dace a kara mai da hankali kan kasuwar kasashe masu tasowa."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China