Wata sanarwar da kakakin kungiyar Mahmoud Afifi ya fitar, ta ruwaito Ahmed Aboul-Geit na kira ga jam'iyyun siyasa a kasar, su shawo kan takkadamar dake tsakaninsu da rarrabuwar kawuna a kasar da yaki ya daidaita.
Ya kuma bayyana fatan al'ummar kasar za su cimma yarjejeniyar da za ta kai ga gudanar da zabuka karkashin sahihan dokoki da kundin tsarin mulki.
Duk da jam'iyyun siyasar kasar sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da MDD ta dauki nauyi a shekarar 2015, har yanzu Libya na fuskantar takkadama tsakanin gwamnatocin dake gabashi da yammacin kasar, inda dukaninsu ke fafutukar samun halacci. (Fa'iza Mustapha)