Taron hukumar yaki da cutar shan-Inna ta Afirka(ARCC) zai gudana ne a birnin Nairobin kasar Kenya daga ranar 12- 16 ga watan Nuwanban da muke ciki, inda za a yi bitar nasarorin da nahiyar ta samu game da kawar da kwayar cutar ta shan-Inna.
Yayin taron, ana saran kasashen nahiyar guda bakwai da suka hada da Kamaru da Najeriya da Guinea-Bissau da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Sudan ta kudu da Equatorial Guinea da Afirka ta kudu za su gabatar da rahoto game da irin matakan da suka dauka na ganin bayan cutar.
Najeriya ce kasa daya tilo a nahiyar da har yanzu ke fama da cutar, yayin da ake kokarin hana yaduwarta a kasashe masu hadari kamar Nijar, da Kenya da Somaliya da Jamhuriyar demokiradiyar Congo.
Wakilin hukumar lafiya ta MDD a Kenya Rudi Eggers, ya yaba da irin ci gaban da kasashen na Afirka suka samu game da kawar da cutar shan-Inna, amma kuma ya jaddada cewa, hanya mafi muhimmanci ta hana sake bullo cutar ita ce kara sanya ido. (Ibrahim)