in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wace irin yanar gizo ake bukata?
2018-11-09 10:50:13 cri

Ana gudanar da babban taron yanar gizo karo na biyar a garin Wuzhen na lardin Zhejiang, inda mahalarta taron suke tattaunawa game da wannan batu, da yadda za a kafa wata duniya dake amfani da fasahar zamani mai aminci ga juna, domin gina kyakkyawar makomar yanar gizo a fadin duniya.

Ya zuwa karshen watan Yunin da ya gabata, gaba daya adadin al'uumun kasashen duniya, wadanda ke samun bayanai daga shafunan yanar gizo ya kai biliyan 4 da miliyan 200, adadin da ya kai kaso 55 bisa dari daga cikin daukacin al'ummun kasashen duniya. Haka kuma hanyoyinsu, na samun ilmomi, da zaman rayuwa, da yin tunani sun sauya sannu a hankali sakamakon shiga yanar gizo.

A don haka, bayanan da ake gabatarwa a kan shafunan yanar gizo suna da muhimmanci matuka, saboda suna yin babban tasiri ga al'umun fadin duniya, shi ya sa dole ne a tabbatar da cewa, ana gabatar da bayanai na gaske bisa doka, kuma bai kamata ba a gabatar da bayanai na jabu. To dai dai alal hakika wasu mutane sun fi son gabatar da bayanan jabu, domin jawo hankalin masu karatu.

Tim Berners-Lee, masanin kimiyya a kasar Birtaniya, wanda ya kafa shafin World Wide Web a shekarar 1989, ya gaya wa manema labarai na kamfanin dillancin labarai na Routers cewa, ya yi bakin ciki matuka ga ci gaban yanar gizo, saboda ya ga wasu manyan kamfanonin yanar gizo suna gudanar da harkokin dake shafar yanar gizo. Masu shiga shafunan yanar gizo suna bayyanawa juna kiyayya, har wasu suna satar bayanai a kan yanar gizon, duk wadannan sun sabawa makasudinsa na kafa yanar gizo shekaru 30 da suka gabata. Yana ganin cewa, kamata ya yi a kara sada zumunci a kan yanar gizo.

Shi ma mataimakin farfesa a jami'ar British Columbia Taylor Owen na ganin cewa, idan ana son gudanar da harkokin yanar gizo lami lafiya, dole ne daukacin kasashen duniya su hada kai, ta yadda za a kafa wani tsari mai oda da adalci.

Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana, duk da cewa, ba a iya ganin hakikanin abubuwa ta yanar gizo kai tsaye da ido, amma masu shiga yanar gizo suna rayuwa a duniya guda ne, a don haka kamata ya yi kasashen duniya su yi kokari tare, domin gina kyakkyawar makomar yanar gizo.

To, ko wace irin yanar gizo muke bukata? Shahararren masanin kimiyya, wanda ya riga mu gidan gaskiya Michael Dertouzos ya taba bayyanawa a shekarar 2001 cewa, kafin shekaru 300 da suka gabata, mun yi wani babban kuskure, wato mun raba fasaha da al'ada, yanzu lokaci ya yi da za a hada su wuri daya.

A takaice dai, ana bukatar amincewa juna, kuma dole kasashen duniya su tsara ka'idojin tafiyar da harkokin dake shafar yanar gizo, bisa tushen amincewa juna, da biyayyar juna, da kuma hakuri da juna.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China