in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta farfado da sayar da furannin hibiscus a kasashen waje
2018-11-09 10:17:40 cri

Gwamnatin Najeriya ta ce, kasar za ta farfado da shirinta na sayar da furannin hibiscus zuwa kasuwannin kasashen waje, hibiscus, wata nau'in ciyawa ce da ake noman ta a kasar, kana furanni ne masu matukar ban sha'awa kuma mafiya daraja a duniya.

Najeriyar na daya daga cikin kasashen duniya mafiya yawan samar da furannin hibiscus. Kasar ta dena fitar da furannin ne tun bayan bayyanar wani rahoto game da bullar wasu kwari da suka addabi furannin a wasu wuraren da aka adana furannin.

Nan da wasu 'yan makonnin masu zuwa, Najeriyar za ta maido da fitar da busasshiyar filawar ta hibiscus a kasashen waje, inda kasar za ta yi amfani da wannan dama wajen samun kudaden muyasa na kasashen waje, da kuma bunkasa hanyoyin fadada tattalin arzikin kasar.

Wasu jami'ai a kasar sun ce, za'a fara girbar furannin na hibiscus a kowanne lokaci daga yanzu. "Manomanmu sun zaku kuma an riga an shirya filayen noman." in ji Vincent Isegbe, jami'ar hukumar aikin gona ta kasar (NAQS).

"Wani labari mai dadi ji shi ne, Najeriya tana da manyan gonakin noma, kuma ana iya noma furannin a kowane lokaci a duk tsawon shekara," Isegbe ta fadawa manema labarai a Abuja.

Furannin hibiscus na kasar Najeriya, wasu nau'ika ne na musamman, suna iya girman tsawon mita 15 da fadin mita 6. Yawanci an fi noma ta ne a jihohi 6 na arewacin kasar, da suka hada da Kano, Katsina, Bauchi, Gombe, Borno, da Jigawa.

Kasar Mexico ta fi kowace kasa sayen furannin hibiscus na Najeriya.

Ana sayar da furannin hibiscus, bayan an busar da su, kana ana sayar da su a kasuwannin kasashen Holland, Jamus, Amurka, da sauran sassan nahiyoyin Turai da Asiya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China