in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Afirka 45 za su halarci taron musamman na 11 na AU
2018-11-09 10:04:03 cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Habasha, ta ce ana sa ran shugabannin kasashen Afirka 45, za su halarci taron musamman na 11 na kungiyar AU, wanda zai gudana a ranekun 17 da 18 ga wata a birnin Addis Ababa.

Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta ce shugabannin za su tattauna game da kudurin nan na yiwa hukumar zartaswar kungiyar ta AU kwaskwarima, da zakulo hanyoyin inganta ayyukan kungiyar, ta yadda za ta iya fuskantar kalubalen da daukacin kasashen nahiyar 55 ke fuskanta, a matakai na shiyyoyi da na kasa da kasa.

Har ila yau, shugabannin za su tattauna game da nasarorin da aka cimma, a fannonin tattalin arziki, da hade kudurorin siyasar nahiyar, kamar yadda aka tsara a ajandar bunkasa nahiyar ta kungiyar AU nan da shekarar 2063.

Gabanin taron shugabannin, manyan ministocin kasashen nahiyar 55, za su gudanar da zama na tsara ajandar taron shugabannin, a ranekun 14 da 15 ga watan nan na Nuwamba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China