in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin ya bukaci al'ummar Afrika su kara hada kai da Sin don samun kyakkyawar makoma
2018-11-08 15:10:05 cri
Jakadan kasar Sin a kasar Botswana Zhao Yanbo, ya bukaci kasashen Afrika da su kara zurfafa mu'amala da kasar Sin domin gina kyakkyawar makoma ga al'ummar nahiyar a nan gaba.

Da yake jawabi a gaban malamai da daliban jami'ar Botswana, jami'in diplomasiyyar na kasar Sin ya jaddada bukatar karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika da kuma Sin da Botswana, kana ya fayyace hanyoyin da za su kara dankon zumunta tsakanin Sin da Afrika.

Ya kara da cewa, kasar Sin ita ce kasa mai tasowa mafi girma a duniya, yayin da Afrika ita ce nahiyar da ta fi yawan kasashe masu tasowa, Zhao ya ce, Sin da Afrika suna da tarihi mai kamanceceniya da juna ta fuskar neman ci gaba, da burin ci gaban siyasa a nan gaba.

Jakadan na Sin ya kara da cewa, bangarorin biyu sun budewa juna kofar yin hadin gwiwa da amfanawa juna mai sigar musamman. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China