in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya jaddada niyya da imanin kara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje
2018-11-08 12:00:08 cri

A kwanan baya, a lokacin da yake rangadin aiki a birnin Shanghai, babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar, kana shugaban kwamitin kolin soja na kasar Xi Jinping ya jaddada cewa, dole ne a mayar da tunani game da tsarin mulkin na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki, a kuma dauki kwararan matakan aiwatar da manufofin da kwamitin kolin jam'iyyar ya tsara, domin tabbatar da tsayawa imani, da niyyar kara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, sannan bisa ka'idar neman ci gaba ba tare da tangarda ba, da aiwatar da sabon tunanin neman ci gaba, da kuma kara yin kwaskwarima kan sana'o'in masana'antu bisa bukatun da ake da su a kasuwa, ta yadda za a iya kafa wani tsarin tattalin arzikin zamani, da kuma hanzarta samar da karfin gogayya mafi muhimmanci ga birnin Shanghai, ta yadda zai iya kara samar da hidima ga ayyukan kwaskwarima da ake yi a sauran yankunan kasar.

A ranakun 6 da 7 ga wata, bayan da ya halarci bikin kaddmar da baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin, da wasu bukukuwan dake da nasaba da bikin, shugaba Xi ya yi rangadin aiki a wasu kamfanoni da masana'antu, da unguwannin mazauna da cibiyoyin daidaita harkokin yau da kullum na birnin, da kuma yankin kimiyya da fasaha na zamani wadanda suke birnin Shanghai.

Babban Ginin Cibiyar Shanghai da tsayinsa ya kai mita 632, gini ne mafi tsayi a kasar Sin, kuma mafi tsayi na biyu a duniya. A shekarar 2007, lokacin da Xi Jinping ya yi aiki a birnin Shanghai, ya taba dudduba shirin gina wannan gini, ya taba neman gina gini mai inganci dake da basirar dan adam da abubuwan da ke shafar rayuwar dan Adam na yau da kullum, kuma ba zai gurbata muhalli ba. A safiyar ran 6 ga wata, wannan gini ya zama zangon farko da shugaba Xi Jinping ya kai ziyara. A dakin bude ido dake bene na 119, Xi Jinping ya kalli kyakkyawan yanayi na birnin Shanghai, inda ya bayyana cewa, bayan da aka kaddamar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, kasar Sin ta samu sauye-sauyen da ba a gani a da ba, birnin Shanghai wani misali ne dake burge mutane.

Mutanen dake zaune a yankin karamar hukumar Hongkou ta birnin Shanghai sun yi yawa sosai, sabo da haka, karamar hukumar Hongkou ta gina rumfuna 35 da dukkan mazauna, musamman tsofaffi wadanda suke zaune a yankin za su iya shiga cikin mintoci 15. A wata rumfar dake renon wasu tsofaffi, wasu tsofaffi suna tsara kayayyaki da hannu. Shugaba Xi ya shiga ya gaishe su.

"Kwamitin kolin jam'iyyarmu na mai da hankali sosai kan matsalolin da tsofaffi suke gamuwa da su, yanzu kasar Sin ta zama al'umma mai tsoffi, sabo da haka, dole ne mu mai da hankali kan yadda tsofaffinmu suke, da lafiyarsu a lokacin da muke mai da hankali kan yadda jama'armu suke jin dadin zamansu. Abubuwan da kuke yi a nan suna da amfani sosai."

Sannan a yammacin ranar 6 ga wata, shugaba Xi Jinping ya kai ziyara cibiyar daidaita harkokin yau da kullum na birni ta yankin Putong, inda ya san yadda ake daidaita harkokin yau da kullum na birnin Shanghai yadda ya kamata. Mr. Xi ya nuna cewa, "Daidaita harkokin yau da kullum muhimmin abu ne dake bayyana karfin mulkin wata kasa a sabon yanayin zaman al'umma ta zamani. Dole ne a yi amfani da fasahohi da dabaru mafiya kwarewa, wajen daidaita harkokin yau da kullum a kasaitaccen birni. Ya kamata a mai da hankali wajen yin amfani da dabarun kimiyya da basirar dan Adam, wajen daidaita harkokin yau da kullum. Ya kamata birnin Shanghai ya ci gaba da neman sabbin dabarun zamani, wajen daidaita harkokin yau da kullum, kamar yadda ya kamata a kasataiccen birnin kamar Shanghai."

A wannan cibiya, Xi Jinping ya kuma kalli yadda ake gina da kuma tafiyar da harkoki a tashar teku ta Yangshan, mai aiki da na'urorin mutum-mutumin basirar dan Adam ta bidiyo, inda ya nuna cewa, idan ana son inganta karfin wata kasa bisa bunkasar tattalin arziki, dole ne a inganta karfinta kan harkokin teku, musamman kan hanyoyin sufurin teku. Idan an kammala gina tashar teku ta Yangshan mai aiki da na'urorin mutumi-mutumin basirar dan Adam, za a iya kafa wani kyakkyawan yanayi, ga kokarin mayar da birnin Shanghai zama cibiyar sufuri ta kasa da kasa, da aikin gina yankin yin cinikayya maras shinge, da kuma kara bude kofar kasar Sin ga waje.

Yankin kimiyya da fasahar zamani na Zhangjiang, cibiyar kirkiro sabbin fasahohin zamani ta Shanghai dake kan matsayin kasa, inda ake da dimbin kayayyakin kimiyya da fasaha na zamani da wasu hukumomin nazarin kimiyya da sabbin fasahohin zamani. A dakin nune-nunen fasahohin zamani, Xi Jinping ya yi hira da wasu masu aikin kimiyya da fasaha, inda ya jaddada cewa, yanzu ilmin kimiyya da fasahohin zamani na amfana wa makomar kowace kasa sosai, har ma na kawo alheri sosai ga zaman rayuwar al'umma. Shugaba Xi ya ce, "Dole ne a kara sanin muhimmancin kirkiro sabbin fasahohin zamani. Sannan dole ne a dauki matakai daban daban, na kara neman ilmin kimiyya, da kirkiro sabbin fasahohin zamani a yanzu. Abubuwan da kuke yi suna da muhimmanci matuka a wannan lokacin da kasarmu ke ciki, da ma kokarin cimma burinmu na farfadowar al'ummar Sinawa, a lokacin cika shekaru dari da kafuwar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da lokacin cika shekaru dari na kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin. Dole ne mu rike wannan dama, mu kara kirkiro sabon yanayi mai kyau ga aikinku na kirkiro sabbin fasahohin zamanin yanzu." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China