in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya yi shawarwari da jagororin hukumomin tattalin arziki na kasa da kasa
2018-11-07 11:13:44 cri

Jiya Talata a nan birnin Beijing, firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya yi shawarwari da jagororin hukumomin tattalin arziki na kasa da kasa guda shida karo na uku, inda Li ya jaddada cewa, kasar Sin tana son yin kokari wajen goyon bayan tsarin gudanar da cinikayya tsakanin bangarori da dama, tare da sassa daban daban, da kuma da kiyaye tsarin cinikayya maras shinge, ta yadda za a kara habaka cudanyar tattalin arzikin duniya, haka kuma kasar Sin za ta dauki matakai masu karfi, domin samun ci gaban tattalin arziki mai inganci sannu a hankali.

A cikin shekaru biyu da suka gabata, an taba gudanar da shawarwari tsakanin sassa bakwai; wato kasar Sin, da hukumomin tattalin arziki na kasa da kasa guda shida har sau biyu, wato sau daya a ko wace shekara, shawarwarin da suka kasance dandalin tattauna tsakanin firayin ministan kasar Sin da jagororin hukumomin tattalin arziki na kasa da kasa. Babban taken shawarwari na bana shi ne: "sa kaimi kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da sauran kasashen duniya domin samun ci gaba tare".

Shugaban bankin duniya Jim Yong Kim, da babbar daraktar asusun ba da lamuni na duniya Christine Lagarde, da babban daraktan kungiyar cinikayya ta kasa da kasa ko WTO Roberto Azevedo, da babban sakaraten kungiyar bunkasa hadin kan tattalin arziki da samar da ci gaba Angel Gurria, da shugaban hukumar samar da daidaito a fannin hada hadar cinikayya Mark Carney, da kuma mataimakiyar babban daraktan kungiyar kwadago ta kasa da kasa Deborah Greenfield sun halarci shawarwarin, inda suka tattauna da firayin minista Li Keqiang, kan yanayin da tattalin arzikin duniya ke ciki a halin yanzu, da yadda ake kiyaye tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, da tattalin arzikin kasar Sin da manufar kasar ta yin kwaskwarima da bude kofa da sauransu, yayin taron, Li yana mai cewa, "Wannan taro yana da ma'ana ta musamman, saboda yanayin tattalin arziki da harkar kudin da kasashen duniya ke ciki ya gamu da manyan sauye-sauye. Game da kasar Sin kuwa, bana take cika shekaru 40 tun bayan fara aiwatar manufar yin kwaskwarima da bude kofa. Kasar Sin tana fatan sauran kasashen duniya za su lura cewa, za ta ci gaba da bude kofa ga ketare, haka kuma za ta kara zurfafa kwaskwarima a cikin gida, yayin da take kokarin ingiza tsarin gudanar da cinikayya dake tsakanin bangarori daban daban, ta yadda za a farfado da tattalin arzikin duniya, tare kuma da samun karuwarsa, bisa tushen hakuri da juna cikin lumana."

Li ya bayyana cewa, kasashen duniya suna fuskantar sabon zaben dake gabansu, kuma kamata ya yi su nace ga manufar bude kofa, da gudanar da cinikayya tsakanin bangarori da dama, ta haka ne za su kara habaka cudanyar tattalin arzikin duniya yadda ya kamata. Muddin dai an gudanar da cinikayya tsakanin bangarori daban daban, ko shakka ba bu za a iya samun wadata, da kuma cimma burin samun karuwar tattalin arziki a fadin duniya, bisa tushen yin hakuri da juna. A don haka kasar Sin tana son yin kokari wajen goyon bayan tsarin gudanar da cinikayya tsakanin bangarori da dama tare da sauran kasashen duniya, tare kuma da kiyaye tsarin cinikayya maras shinge, yana mai cewa, "Yayin taron da muke gudanarwa, mun kara fahimtar hakikanin yanayin da kasashen duniya ke ciki yanzu, haka kuma mun sanar da cewa, za mu ci gaba da kiyaye tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, da tsarin cinikayya maras shinge. Nan gaba za mu kara tattaunawa domin kara zurfafa fahimtar juna. Kasar Sin tana adawa da tsarin cinikayya bisa bangare guda, da tsarin ba da kariya ga cinikayya, tana kuma fatan yin kokari tare da sauran sassan duniya, domin neman samun dabarar daidaita matsalaloli bisa tushen nuna biyayya ga juna da daidaito."

Kana Li ya yi bayani kan yanayin tattalin arzikin da kasarsa ke ciki, inda ya yi nuni da cewa, ana gudanar da tattalin arzikin kasar yadda ya kamata, kuma nan gaba za ta dauki karin matakai masu karfi, domin samun ci gaban tattalin arziki mai inganci sannu a hankali a kasar, ya ce, "Kasar Sin ta nunawa jagororin hukumomin tattalin arziki na kasa da kasa da suke halartar taron cewa, za ta ci gaba da aiwatar da manufofin hada hadar kudi masu dacewa, haka kuma za ta kara rage haraji. A sa'i daya kuma, za ta kara saukaka ayyukan hukumomin gwamnatin kasar, domin kyautata muhallin kasuwanci a kasar."

A nasu bangare, jagororin hukumomin tattalin arziki na kasa da kasa sun bayyana cewa, babban sakamakon da kasar Sin ta samu a cikin shekaru 40 da suka gabata, ya samar da babbar moriya ga al'ummun daukacin kasashen duniya, kuma hukumomin tattalin arziki na kasa da kasa sun son kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu da kasar Sin, domin dakile kalubale tare. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China