in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A lokacin da ake bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya, kafofin watsa labarai na kasa da kasa da masana masu ba da shawara za su taka muhimmiyar rawa
2018-11-06 11:45:21 cri

Da safiyar jiya Litinin ne aka kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin na kasa da kasa CIIE karo na farko a birnin Shanghai. Wannan wani muhimmin mataki ne dake bayyana yadda kasar Sin take kara inganta bude kofarta, da niyya da imanin kasar wajen kara bayar da gudummawa ga kokarin bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya. Kafofin watsa labaru na kasa da kasa da masana masu ba da shawara dukkansu, na ganin cewa, a lokacin da ake kokarin bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya, za su taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ganin an kafa wani tsarin raya tattalin arzikin kasa da kasa cikin adalci ta hanyar bude kofa.

Bisa ajandar wannan biki na CIIE, da yammacin jiya an shirya wani taron tattaunawa na Hongqiao, inda kafofin watsa labarai da masana masu ba da shawara suka halarta, inda suka tattauna kan yadda za su iya taka rawa a lokacin da ake kokarin bunkasa tattalin arzikin kasa da kasa ta hanyar bude kofa.

Mr. Grzegorz W Kolodko, tsohon mataimakin firaministan kasar Poland ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, kasashen duniya na dogaro da juna suna cin moriya tare. Don haka, bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya, ya zama abin da ake yi kuma ba a iya canza shi ba, sabo da haka, yanzu ana bukatar shirin daidaita wasu matsaloli masu tsanani cikin gaggawa. Mr. Grzegorz W Kolodko yana mai cewa, "A hakika dai, yanzu ba a amince da bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya kamar yadda ya kamata ba, wasu shirye-shiryen da wasu masana da hukumomi masu ba da shawara suka gabatar ba su yi aiki kamar yadda ake fata ba. A ganina, yanzu muna fatan kasar Sin ta fitar da sabuwar dabarar daidaita matsalolin. An yi hasashen cewa, ba za a iya canza kokarin bunkasa duniya baki daya ba, muna bukatar daidaita manufofi da matakan daidaita harkokin kasa da kasa da kasashen daban daban suka gabatar. Na yi imanin cewa, tabbas kasar Sin za ta taka muhimmiyar rawa a wannan fanni."

A bana ake cika shekaru 40 da kasar Sin ta kaddamar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga waje. A cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin da sauran kasashen duniya sun samu ci gaba da bunkasuwa tare. A matsayin kungiyar tattalin arziki mafi gima ta biyu a duk duniya, yanzu kasar Sin na kara samun ci gaba lami lafiya, har ma ta kasance tamkar wani muhimmin injin dake ciyar da tattalin arzikin duk duniya gaba. Mr. Dominique de Villepin, tsohon firaministan kasar Faransa ya ce, a lokacin da saurin ci gaban tattalin arzikin kasashen duniya ya ragu, kara yin hadin gwiwar a zo a gani tsakanin kasa da kasa yana da muhimmanci. Shawarar bunkasa "ziri daya da hanya" da kasar Sin ta gabatar ta kasance abin koyi. Mr. de Villepin ya bayyana cewa, "Shawarar bunkasa 'ziri daya da hanya daya' da shugaba Xi Jinping ya gabatar a shekarar 2013 ta zama abin koyi wajen samar da ayyukan more rayuwa, wadanda za su shafi kasashe da yankuna fiye da 60 tare da jarin kudade wajen dalar Amurka biliyan 900 da za a zuba wa wasu muhimman ayyukan more rayuwar al'umma. Sabo da kasancewar wannan shawara a duniya, kasashen Turai da Amurka ma za su samar da irin wadannan ayyuka."

A lokacin da ake kokarin kafa tsarin tattalin arziki dake bude kofa ga duk duniya, kafofin watsa labarai suna taka muhimmiyar rawa wajen neman samun ra'ayi daya daga al'ummomi daban daban. Mr. John Micklethwait, babban editan Bloomberg News, yana ganin cewa, ko da yake, bunkasa tattalin arzikin duniya ya kasance kamar wata ka'idar da ake bi a halin yanzu, har yanzu wasu suna adawa da ita, har ma suna daukar matakan yakar wannan ka'ida. Sakamakon haka, yanzu takkadamar da ake yi a fannin cinikayya da matakin kare zuba jari sun tsananta, kokarin bunkasa tattalin arzikin duniya na fuskantar kalubale mai tsanani. Ya ba da misalin cewa, a lokacin da kasar Sin take bude kofa kuma take bunkasa tattalin arziki cikin 'yanci, kafofin watsa labaru na taka rawa sosai, yanzu rahotonnin da aka bayarwa game da kasar Sin na zama rahotonnin dake shafar duk duniya. Mr. John Micklethwait ya ce, "Kamar yadda ake zana wani zane, idan ba mu san hakikanan abubuwa ba, shi ke nan, za mu yi amfani da launi iri daya kadai. Amma kasar Sin ta samu kyakkyawan sakamako wajen yin mu'amala da sauran kasashen duniya. Yawan tarukan yada labaru da wakilanmu dake kasar Sin suka halarta ya ninka sau 3. A hali mai sarkakiya da ake ciki a duk duniya a yanzu, a ganina, kara yin mu'amala da sauran kasashen duniya yana da muhimmanci matuka."

Wannan baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin na kasa da kasa karo na farko ya jawo hankulan kafofin watsa labaru na kasar Sin da na sauran kasashen duniya. Mr. Shen Haixiong, shugaban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin CMG wanda ya kuma halarci wannan taron tattaunawa, ya bayyana cewa, yanzu sauran kasashen duniya na mai da hankali kan ra'ayoyin da kasar Sin ta gabatar, wannan ya bayyana cewa, nuna goyon baya ga ra'ayin daidaita batutuwa tsakanin bangarori daban daban, da yin cinikayya ba tare da shinge ba, su ne muhimman ra'ayoyin da galibin kasashen duniya suke amincewa.

Wakilan kafofin watsa labaru da masana masu ba da shawara sun bayyana cewa, dole ne a san wace ka'ida ce duk duniya ke bi, da kuma inda duniya ta dosa. Ya kamata su taka karin rawa wajen bunkasa tattalin arzikin ta hanyar bude kofa ga duk duniya baki daya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China