in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin AFDB: Taron zuba jari na Afrika zai taka muhimmiyar rawa wajen samar da kudaden raya nahiyar
2018-11-06 10:54:43 cri
An bayyana taron zuba jari na Afrika dake karatowa, a matsyain wanda zai taka rawa gaya, wajen samar da biliyoyin dalolin da ake bukata na samar da kayayyakin more rayuwa da na ci gaba da ake bukata a nahiyar Afrika.

Daraktan sashen yada labarai na bankin raya Afrika AFDB, Victor Oladokun, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, a kowacce shekara, nahiyar Afrika na samun gibin kudin jari na dala biliyan 130-170, wanda rabinsa shi ne gibin kudin samar da ababen more rayuwa da ake son a cike.

Za a fara taron ne daga gobe Laraba zuwa ranar Juma'a, a birnin Johannesburg. Kasuwannin hannayen jari da masu zuba jari da bankunan hadin gwiwa na raya kasashe da sauran abokan hulda daga bangarori masu zaman kansu mahalarta taron, za su lalubo tare da cimma yarjeniyoyin da darajarsu ta kai biliyoyi domin cimma bukatun nahiyar.

Victor Oladokun, ya bayyana taron a matsayin hanyar jan jari zuwa Afrika. Inda ya ce sun bullo da shi ne domin nahiyar na bukatar rungumar sabbin hanyoyin samun kudi. Ya kuma yi ammanawa cewa, ba taron shan shayi za a yi ba, domin bankin AFDB, zai sanar da ingantattun yarjejeniyoyi a karshen taron. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China