in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hamas ta sha alwashin ci gaba da nuna kin jinin Isra'ila har sai hakarta ta cimma ruwa
2018-11-06 10:58:32 cri
Wani babban jami'in kungiyar fafutukar Islama ta Hamas ya sanar a jiya Litinin cewa, za su ci gaba da yin zanga zangar nuna kin amincewa da manufofin Isra'ila har sai sun cimma burinsu.

Issam Daalees, daya daga cikin shugabannin kungiyar Hamas dake tsakiyar zirin Gaza, shi ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwar da aka rabawa manema labarai.

Da yake tsokaci game da yunkurin shiga tsakani wanda hukumar tattara bayanan sirri ta kasar Masar ke yunkurin shiryawa, Daalees ya ce za'a ci gaba da yin wancan yunkurin shi ma "har sai mun kai ga cimma matsaya wadda ta yi daidai da muradun al'ummarmu."

Tun da farko a wannan rana, wata tawagar wakilan Misrawa ta isa zirin Gaza ta hanyar Erez wadda ta ratsa kasar Isra'ila domin maido da tattaunawar sulhu da bangarorin Palastinawa dangane da batun yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila.

Wata kafar yada labarai ta cikin gida ta ce, wakilan sun gudanar da tattaunawa tare da wasu manyan jami'an kungiyar Hamas da sauran shugabannin daya bangaren domin cimma matsaya na duba yiwuwar tsagaita bude wuta tsakanin Isra'ila da mayakan kungiyar Hamas a zirin Gaza. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China