in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guinea ta yabawa sahihiyar dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika
2018-11-03 15:21:28 cri

Ministan makamashi da ruwa na kasar Guinea, Cheick Taliby Sylla, ya ce kasar Sin sahihiyar abokiyar hulda ce ga kasashen Afrika, a daidai lokacin da kasashen ke kokarin shawo kan gibin wutar lantarki da bunkasar tattalin arziki.

Da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua yayin ziyararsa ta baya-bayan nan a Yaounden Kamaru, ministan ya ce shirin samar da wutar lantarki na GEI da kasar Sin ta gabatar, zai taimakawa Afrika shawo kan matsalolin lantarki da raya tattalin arziki.

Global Energy Interconnection GEI, shiri ne da kasar Sin ta gabatar a shekarar 2015, da nufin samar da hadakar turakar lantarki mai karfi da inganci, wanda zai kasance wani dandalin samar da ingantacciyar ci gaba da amfani da makamashi mai tsafta a fadin duniya.

Ya ce, batun wutar lantarki, ya shafi harkokin samun ci gaba da kyautata yanayin rayuwar al'umma.

Ya kuma yabawa kasar Sin a matsayinta na babbar kasa da take taimakawa Afrika wajen samar da bakin zaren samun ci gaba mai karko.

Ministan ya ce, wasu na ganin kasar Sin na jefa Afrika cikin kangin bashi, yana mai cewa, a ganinsa, dukkan hukumomin Afrika ba su amince da hakan ba, domin Sin taimakonsu take wajen samar da kayayyakin more rayuwa da za su kai ga samar da ci gaban tattalin arziki da inganta rayuwar al'ummar nahiyar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China