in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arziki mai zaman kansa na kokarin habaka sabuwar kasuwa ta sabbin masana'antu a kasar Sin
2018-10-31 17:23:27 cri

Bisa yanayin da ake ciki na koma bayan saurin ci gaban tattalin arzikin duniya, da fuskantar takaddamar cinikayya, yanzu raya sabbin masana'antu na kasancewa muhimman tsare-tsare na kasashe daban daban wajen nuna sabon fiffikonsu a duniya. A yayin da ake yin irin wannan takara, tattalin arziki mai zaman kansa yana ta mai da hankali sosai kan sauyin bukatun kasuwanni na gida da na waje, da kuma bukatun su a cikin 'yan shekarun da suka gabata, da nufin neman habaka sabuwar kasuwa a sabbin masana'antu, tare kuma da ciyar da tattalin arzikin kasar ta Sin gaba yadda ya kamata.

Tabbatar da samun ci gaban tattalin arziki mai inganci, ba manufa ce da kasar Sin ke bi a yanzu haka kawai ba, ta kasance hanya ce ta dole da kasar ke bi don kara matsayinta na wata babbar kasa a fannin tattalin arziki zuwa na wata babbar kasa mai karfi a fannin tattalin arziki. Idan aka kwatanta da manyan tsare-tsare na samun bunkasuwa na wasu kasashe masu ci gaba, kamar su manyan tsare-tsare na fasahohin zamani nan da shekarar 2020 na kasar Jamus, da shirin manyan tsare-tsare na masana'antun kire-kire na zamani na kasar Amurka, da shirin masana'antu na nan gaba na kasar Faransa da dai sauransu, kullum kasar Sin na dora muhimmanci kan sabbin fasahohi, da bin masana'antu, da sabon yanayin sana'o'i da kuma sabon tsari da dai sauransu don karfafa karfinta na yin takara.

A shekaru biyu da suka gabata, kasar Sin ta gabatar da shirin bunkasa sabbin masana'antu masu muhimmanci cikin shekaru biyar masu zuwa, kuma bisa ga shirin, ya zuwa shekarar 2000, yawan darajar sabbin masana'atu masu muhimmanci a kasar zai karu zuwa 15% na adadin GDP na kasar, wadanda za su kafa sabbin ginshikai biyar ta fannonin fasahar sadarwa da ayyukan kera na'urorin zamani da nazarin halittu da kiyaye muhalli da kuma kirkire-kirkire na zamani, wadanda kuma za su kara samar da guraben ayyukan yi ga mutane sama da miliyan guda a kowace shekara.

Shirin dai ya samar da kyawawan sauye-sauye ga tattalin arzikin kasar ta Sin. Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar ta bayar sun yi nuni da cewa, a farkon watanni bakwai na wannan shekara, yawan darajar sabbin masana'antu masu muhimmanci ya karu da 8.6% bisa na makamancin lokacin bara, musamman ma motoci masu aiki da sabbin makamashi da mutum-mutumin inji dake taimakawa ga ayyukan masana'antu. A sauye-sauyen da ake gudanar kuma, kamfanoni masu zaman kansu sun taka rawa mai matukar muhimmanci.

Bisa alkaluman da aka samu, an ce, kamfanoni masu zaman kansu suna da ikon mallakar fasahohi kaso 65 bisa dari, da kirkire-kirkiren fasahohi kaso 70 bisa dari, da sabbin kayayyaki kaso 80 bisa dari a kasar Sin. Rukunin WPP na kasar Birtaniya ya taba fitar da wani jerin sunayen alamomin mallakar kayayyaki 100 mafiya daraja na kasar Sin, inda aka nuna cewa, a shekarar 2014, darajar alamomin mallakar kayayakin kamfanonin gwamnatin kasar Sin dake cikin alamomin mafiya daraja 100 a kasar ta kai kaso 71 bisa dari, amma ya zuwa shekarar 2018, darajar ta kai kaso 40 bisa dari kawai, a akasin haka, darajar alamomin kayayyakin kimiyya da fasaha da sayayyar kayayyaki na kamfanoni masu zaman kansu sun karu cikin sauri, kamfanonin da suke gudanar da harkokinsu ta hanyar yin kirkire-kirkire, kimiyya da fasaha, suna taka rawar gani ga ci gaban alamomin mallakar kayayyakin kasar Sin, haka kuma sun daga matsayin kasar Sin a fadin duniya.

Idan an waiwayi tarihin kasar Sin a cikin shekaru 40 da suka gabata, za'a lura cewa, tattalin arziki mai zaman kansa na kasar ya samu ci gaba cikin sauri bisa mataki na farko, daga baya ya samu ci gaba mai inganci, a halin yanzu yana sa kaimi matuka kan ci gaban tattalin arzikin kasar ta Sin, misali kamfanin Huawei wanda ke kan sahun gaba a cikin kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin ya zuba jarin da yawansa ya kai yuan biliyan 90 domin yin nazari kan fasaha, a sanadin haka kamfanin ya samu kudin shiga sama da yuan biliyan 600, kana kamfanin BYD ya samu jari daga kamfanin Daimler na kasar Jamus har ya kai sahun gaba a kasar Sin wajen kera motoci masu aiki da makamashi mai tsabta, wato ya kera mota mai inganci ta farko a shekarar 2012, yanzu haka ya kera mota mai aiki da wutar lantarki na samfurin Denza 500.

A cikin kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin guda 500 mafiya ci gaba na kasar Sin, yawan kamfanonin kere-kere ya fi na bada hidima har ninki biyu, wannan ya shaida cewa, kamfanoni masu zaman kansu sun samu muhimmin matsayi a sha'anin kere-kere na kasar Sin, kana akwai kyakkyawar makoma kan sha'anin bada hidima a nan gaba. Karuwar yawan mutanen da suka samu matsagaitan kudin shiga, da karuwar yawan tsofaffin mutane a kasar, da sabuwar kwaskwarima kan fasahohi da sana'o'i a fannonin fasahohin halittu da sadarwa, da damar da aka kawo bisa tunanin samun bunkasuwa ba tare da gurbata yanayi ba za su bude sabuwar kasuwa ga kamfanoni masu zaman kansu a fannonin sayar da kayayyaki ta intanet, da sha'anin fasahohin zamani, da sha'anin bada hidima ga tsofaffi da sauransu.

Game da matsalolin da kamfanoni masu zaman kansu suke fuskanta, shugabannin kasar Sin sun gabatar da ra'ayoyinsu, inda suka jaddada cewa, raya tattalin arziki mai zaman kansa shi ne tsarin tattalin arzikin Sin na tushe, kana idan ba a nuna goyon baya ga raya kamfanoni masu zaman kansu ba, akwai matsala kan matsayin siyasa, tilas ne a gyara wannan ra'ayi maras dacewa. Bisa wannan hali, kasar Sin ta gabatar da wasu manufofin kudi da haraji da hada-hadar kudi, ciki har da babban bankin kasar ya kara samar da rancen kudi da ya kai Yuan biliyan 150 don nuna goyon baya ga kamfanoni masu zaman kansu da su tattara kudi, da kuma kamfanonin hannayen jari 11 sun gabatar da shirin sarrafa kudi Yuan biliyan 100 don nuna goyon baya ga bunkasuwar kamfanoni masu zaman kansu.

Bunkasuwar kamfanoni masu zaman kansu a kasar Sin ta shaida tunanin yin kokari na musamman na jama'ar kasar Sin. Yayin da ake kokarin raya tsarin tattalin arziki na zamani, 'yan kasuwa na kamfanoni masu zaman kansu za su ci gaba da yin kirkire-kirkire da yin kokari don kara samar da sabuwar kasuwa ga sabbin sana'o'i. (Bilkisu Xin, Lubabatu Lei, Jamila Zhou, Zainab Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China