"Zuwa karshen wannan makon, zamu tura sama da dakarun sojoji 5,200 zuwa kudu maso yammacin iyakar kasarmu," janar Terrence O'Shaughnessy, kana kwamandan hukumar tsaron sararin samaniyar arewacin Amurka ne ya sanar da hakan a taron manema labarai da yammacin jiya Litinin.
Janar din yace, a yanzu haka kusan dakarun sojojin Amurka 800 sun kama hanyarsu ta zuwa jahar Texas domin tabbatar da tsaron kan iyakar kasar. (Ahmad)