Wata sanarwa da ma'aikatar tsaron kasar ta fitar, ta ce dakarun da aka tura yankin kudancin kasar na Bordj Badji Mokhtar, dake kusa da iyakar kasar da Mali ne suka gano dimbin makaman.
Makaman sun hada da tankokin kakkabo makami mai linzami 4 da babbar bindiga kirar Machine Gun da wasu bindigogi masu kwarya-kwaryar sarrafa kai da gurneti 2 da alburusai 2,984 nau'ika daban daban.
Sanarwar ta ce aikin ya nuna irin jajircewa da sa ido na dakarun da aka tura kan iyaka, domin tabbatar da tsaron yankunan kasar da kuma dakile duk wani yunkuri na fasakaurin makamai ko yi wa tsaro da zaman lafiyar kasar tarnaki. (Fa'iza Mustapha)