in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An karrama basine Mo Yan da lambar yabo ta girmamawa a kasar Algeria
2018-10-30 10:08:55 cri

A ranar Litinin aka baiwa wani basine marubuci Mo Yan lambar yabo ta kasar Algeria ta girmama wanda aka fi sani da "El Athir" saboda kokarinsa da kuma girmama al'adun Sinawa.

Firaiministan Algeria Ahmed Ouyahia, shine ya gabatar da lambar yabon a madadin shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika, a yayin da kasashen Algeria da Sin ke bikin murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya, da kuma kaddamar da bikin baje kolin litattafai na Algeria ta kasa da kasa wanda kasar Sin ce babbar bakuwa ta musamman a wajen bikin.

Mo, mai shekaru 63 da haihuwa, shine ya lashe lambar yabo ta MDD ta Nobel kan rubuce rubuce a shekarar 2012. A ranar Talata, zai gabatar da wata lacca a taron bikin baje kolin litattafai na kasa da kasa a birnin Algiers.

A jiya Litinin aka bude bikin baje kolin, wanda ya samu halartar marubuta na cikin gida dana kasashen waje sama da 1,000 daga kasashe da yankunan duniya kimanin 47. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China