in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai kyakkyawar makoma a yankin Guangdong da Hong Kong da Macau
2018-10-29 19:35:15 cri

Yankin Guangdong da Hong Kong da Macau da ake ginawa a halin yanzu, ya hada da birane 11 na Hong Kong, da Macau, da Guangzhou, da Shenzhen da sauransu, wanda ke bunkasa ayyukan kamfanonin fasahohin zamani, da samar da kayayyaki a lardin Guangdong, da sha'anin ba da hidima, kamar hada-hadar kudi, da dokoki, da zirga-zirgar jiragen sama na yankin Hong Kong, da kuma cibiyar yawon shakatawa ta duniya ta Macau.

Wadannan yankuna suna sa kaimi ga shigar da aikin raya yankin Hong Kong, da Macau, cikin kwaskwarimar da ake yi, ta samun ci gaba a dukkan kasar Sin, kana za a sa kaimi ga babban yankin kasar Sin, ta yadda zai kara bude kofa ga kasashen waje ta yankin Hong Kong da Macau, da kafa babban tsarin bude kofa ga kasashen waje na kasar Sin a sabon zamani.

Akwai mutane fiye da miliyan 68 a yankin Guangdong da Hong Kong da Macau. A matsayin sa na daya daga cikin rukunin manyan birane na duniya, yawan GDP na wannan yanki ya kai dala biliyan 1500, wanda ya yi kamar da kasar Koriya ta Kudu, kana ya zarce na kasar Australia. Haka kuma, wannan yanki zai zama yanki na hudu na yin kirkire-kirkire, da samar da kayayyaki mafiya kyau a duniya bayan yankin New York, da yankin San Francisco, da kuma yankin Tokyo.

Babbar gada a tsakanin Zhuhai da Hong Kong da Macau, da jiragen kasa mafi sauri a tsakanin Guangzhou da Shenzhen da Hong Kong, ta sa kaimi ga raya wannan yanki. Bayan da aka bude babbar gadar, tsawon lokacin da aka kwshewa a hanyar motoci tsakanin Hong Kong da Macau ya ragu, daga awoyi fiye da 3 zuwa rabin awa. Kana idan aka hau jirgin kasa mafi sauri a tsakanin Guangzhou da Shenzhen da Hong Kong, tsawon lokacin da za a kwashe tsakanin Shenzhen da Hong Kong ba zai wuce mintuna 14 ba, har ila yau tsawon lokacin a tsakanin Guangzhou da Hong Kong bai wuce mintuna 47 ba.

Ana iya samun babbar moriya daga hadin gwiwar dake tsakanin yankunan uku, wato lardin Guangdong da yankin Hong Kong da kuma yankin Macau. Bisa labarin da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya bayar, an ce, tun bayan da babbar gadar Hong Kong-Zhuhai-Macau ta fara aiki, babbar motar dakon masu yawon shakatawan da suka isa filin wasan Disney dake Hong Kong daga babban yankin kasar Sin, tana bukatar kusan mintoci goma ne kawai, idan an bi ta kan gadar, hakan ya sa kaimi ga ci gaban filin wasan matuka. Ko shakka babu, Disney wuri ne daya tilo, a cikin kamfanoni da dama da za su samu moriya daga hakan, musamman ma mazauna yankunan nan uku, wadanda suke kokarin gina gudajensu dake yankunan. Alal misali, mazauna yankunan Hong Kong da Macau wadanda suka samun izinin zama a babban yankin kasar, suna iya samun aikin yi, da amfani da tsarin ba da tabbaci ga zaman rayuwa, da inshurar likitanci da sauransu a lardin Guangdong na kasar.

A yankunan nan uku, babu matsala a yi amfani da manyan gine-gine tare, amma akwai wahala mazauna, da kamfanonin yankunan su more zaman rayuwa, ko kuma gudanar da hadin gwiwa tsakaninsu ta hanyar da ta dace, wato ana sa ran za su yi zaman jituwa tare yadda ya kamata.

Kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki a lardin Guangdong, inda ya bukaci lardin da ya nuna kwazo da himma kan aikin gyaran fuska, ta yadda zai samu karin fasahohi bisa dogaro da fifikon sa. Xi ya bayyana cewa, ya dace a ciyar da yankunan Guangdong da Hong Kong da Macau gaba, domin su kasance abin koyi ga sauran yankunan fadin lardin na Guangdong baki daya.

Haka kuma, ci gaban yankunan Guangdong da Hong Kong da Macau, ba ma kawai zai kara hada Hong Kong da Macau da babban yankin kasar wuri guda ba ne, har ma zai samar da karin damammakin bunkasa ga babban yankin kasar, yayin da yake kokarin yin kwaskwarima, da kuma bude kofa ga kasashen ketare. A sa'i daya kuma, zai kara sa kaimi ga ci gaban tattalin arziki a yankin dake gabar kogin Zhujiang; wato za a gina wani sansanin kirkire-kirkiren kasa da kasa, wanda ke kumshe da sabbin ilmomi, da sabbin kimiyya da fasaha, da sabbin fasahohin kera na'urori a yankin. (Zainab Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China