in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama a zirin Gaza ya hallaka yara Palestinawa 3
2018-10-29 10:14:16 cri
Wasu yaran Palestinawa 3 aka kashe a daren ranar Lahadi a wani hari ta sama da Israila ta kai a kan iyakokin yankunan gabashin Khan Younis dake kudancin zirin Gaza, wata majiya daga cibiyar kula da lafiya ce ta ba da rahoton.

Hukumar bada agajin gaggawa ta Palestinian Red Crescent ta sanar a wani gajeren rubutattcen sako wanda ta turawa 'yan jaridu cewa, tagawar jami'an bada agajin lafiya sun kwashe gawawakin mutanen 3.

Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce mutanen uku da aka kashe 'yan shekaru 12 zuwa 14 ne, kuma an kwashe gawawakinsu zuwa asibintin garin Nasser.

Kafafen yada labaran Isra'ila sun bayyana cewa, Palestinawan 3 suna kokarin binne wasu boma bomai ne a gefen titi a tsakanin kan iyakar gabashin zirin Gaza da Isra'ila, sun kara da cewa harin makamai mai linzami ne ya fada kansu kuma ya yi ajalinsu.

Wani bafalastine da ya ganewa idonsa faruwar lamarin ya ce, dakarun sojojin Isra'ila ne suka bude wuta kan tawagar Palestinawa masu aikin jin kai na kiwon lafiya da motar daukar marasa lafiya, domin hana su samun damar isa yankin da aka kaddamar da hare haren ta sama. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China