in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya yi tir da harin da aka kai wa jami'an wanzar da zaman lafiya a Mali
2018-10-28 15:52:50 cri

Kwamitin sulhu na MDD, ya yi tir da harin da aka kaiwa jami'an wanzar da zaman lafiya na majalisar a Mali, wanda ya yi sanadin mutuwar sojoji 2 tare da jikkatar wasu da dama.

Kakakin MDD Stephane Dujarric, ya ce harin da aka kai kan wani sansanin MDD dake wajen Timbuktu, ya yi sanadin mutuwar jami'ai biyu 'yan Burkina Faso da raunatar wasu 11, haka zalika wasu jami'an wanzar da zaman lafiya 4 'yan kasar Togo sun jikkata a wani harin da aka kai musu a kusa da garin Konna dake yankin Mopti.

Cikin wata sanarwa, mambobin kwamitin sulhun sun bayyana damuwa game da yanayin tsaro a Mali da barazanar ta'addanci a yankin Sahel, suna masu kira ga bangarori masu ruwa da tsaki a Mali, su aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da sulhu a kasar ba tare da wani jinkiri ba.

Har ila yau, mamabobin sun jadadda cewa, irin wannan aikin na mugunta ba zai gurgunta kudurinsu na mara baya ga zaman lafiya da sulhu a Mali ba.

Shi ma sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya yi tir da harin na Mali, yana mai cewa, hari kan jami'an wanzar da zaman lafiya laifin yaki ne karkashin dokokin kasa da kasa, kuma dole ne a tabbatar da hukunta wadanda ke da hannu.

Antonio Guterres ya kuma jadadda goyon bayan MDD ga gwamnati da al'ummar Mali da kuma kudurinta na mara baya ga kokarin wanzar da zaman lafiya a kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China