in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron kolin bangarori 4 na Turkiyya ya bukaci a tsakaita bude wuta a Syria
2018-10-28 15:47:56 cri

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya fada a jiya Asabar cewa, taron kolin kasashe hudun da aka gudanar a Turkiyya ya nemi a aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar tsakaita bude wuta domin kawo karshen zubar da jini a Syria.

"Mun samu kyakkyawa kuma tuntuba ta gaskiya a lokacin taron kolin," Erdogan ya bayyana hakan ne a taron hadin gwiwa na kasashen 4 da aka gudanar a Istanbul.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, da shugaban Faransa Emmanuel Macron, sun halarci taron kolin wanda shugaban kasar Turkiyya Erdogan ya karbi bakuncinsa, da nufin tattauna hanyoyin neman kawo karshen rikicin siyasar kasar Syria da kuma samun dawwamamman zaman lafiyar kasar.

Erdogan ya ce, shugabannin mahalarta taron sun bukaci a gaggauta kammala aikin kwamitin tsara kundin mulkin kasar ta Syria nan ba da jimawa ba.

Ana sa ran zuwa karshen wannan shekarar kwamitin shirya dokokin kundin tsarin mulkin kasar zai kammala aikinsa, in ji Putin

A sanarwar hadin gwiwar da shugabannin hudu suka fitar, sun ba da tabbacin nuna cikakkiyar adawa game da yin amfani da makamai masu guba daga dukkan bangarori a Syria.

A nasa bangaren, Macron ya ce, yin amfani da makamai masu guba a dukkan yankunan kasar, ko kuma sauran yankuna na duniya, abu ne da ba za'a amince da shi ba.

Merkel ta gabatar da bukatar daukar matakan da za su tabbatar da warware rikicin siyasar kasar wanda hakan zai tabbatar da samun ingantaccen zabe mai adalci a Syriar, da zai baiwa dukkan bangarorin kasar damar shiga harkokin zaben, cikin su har da 'yan kasar dake ketare.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China