in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika na bukatar gagarumin ci gaba don fitar da miliyoyin mutane daga kangin talauci
2018-10-28 15:19:34 cri

Wani sabon rahoton nazarin yanayin kasashe na 2017-2018, ya ce duk da dimbin ci gaban da kasashen Afrika suka samu cikin shekaru 20 da suka gabata, za a dauki lokaci mai tsawo ana samun ci gaba kafin fitar da dimbin al'umma daga kangin talauci.

Rahoton wanda aka wallafa a matsayin wani bangare na taron tarayya Afrika AU da aka yi a birnin Addis Ababa daga ranar 24 zuwa 26 ga wata, ya kuma nuna cewa, duk da raguwar talauci a nahiyar, har yanzu akwai adadi mai yawa na mutane da ke fama da shi.

Rahoton ya jadadda cewa, saboda tabarbarewar yanayin rayuwa a Afrika cikin shekarun da suka gabata, ana bukatar lokaci mai tsawo na raya nahiyar domin kawar da talauci a tsakanin mafi yawan al'ummar nahiyar.

Ya kuma bukaci a gabatar da shirye-shiryen kare al'umma a nahiyar, yana mai cewa, ci gaba kadai ba zai isa wajen cimma burin nahiyar na rage yunwa da talauci ba, har ma da ajandar da ake son cimmawa ya zuwa 2063. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China