in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin Isra'ila ta jefa dimbin boma-bomai kan sansanonin soji dake zirin Gaza
2018-10-27 21:02:49 cri
A yau Asabar ne kakakin rundunar sojin Isra'ila Jonathan Conricus ya ce, daga tsakar daren jiya zuwa sanyin safiyar yau, an harba rokoki 34 daga zirin Gaza zuwa kudancin yankin Isra'ila, sakamakon haka, sojojin Isra'ilar suka mayar da martani, inda suka jefa dimbin boma-bomai kan sansanonin soji 87 da kungiyar Hamas ta gina a zirin Gaza.

Kawo yanzu, kungiyar Hamas ba ta ce komai ba kan wannan batun.

Sannan a yau ne, kungiyar Jihadi ta Palesdinu ta sanar da cewa za ta tsagaita bude wuta kan Isra'ila, domin magance tsanantan halin da ake ciki a zirin Gaza. Sai dai kuma da a yau din ne, dakarun Quds, wato wani sashen dake karkashin kungiyar Jihadi ya sanar daukar alhakin harba rokoki zuwa kudancin yankin Isra'ila. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China