in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Kokarinta Na Gyare-gyare A Gida Da Bude Kofa Ga Kasashen Waje
2018-10-26 14:00:33 cri

A kwanakin nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping yana rangadi a lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, inda aka fara daukar manufar gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, inda shugaban ya furta cewa, kasar Sin za ta zurfafa gyare-gyaren da take yi, da kara bude kofa ga kasashen waje, kuma tabbas kasar za ta kara samun ci gaba wanda zai ba mutanen duniya mamaki.

La'akari da sauye-sauyen yanayin da ake samu a duniya, rangadin da shugaban kasar Sin ya yi a wannan karo, da furucin da ya yi, dukkansu sun aike da wani sako ga duniya, wato duk da cewa yanayin na da sarkakiya, kasar tana da cikakken imanin daukar matakai na musamman don ci gaba da daukar manufar gyare-gyare da bude kofa, da nufin kara samar da wani yanayi na tabbas da kwanciyar hankali ga duniya.

Hakika sauyin yanayin da ake samu a duniya yana da tasiri matuka, wanda aka dade ba a ga irinsa ba. Da farko, yadda kasashe daban daban ke kara taka rawa a duniya, da dunkulewar tattalin arzikin kasa da kasa, sun sa ana samun sauyawar tsarin siyasa da tattalin arziki a duniya, kana kasashe daban daban suna gudanar da gyare-gyare don neman samun karin ci gaba. Ban da wannan kuma, manufar daukar matakai bisa ra'ayin kashin kai ta sa ana kara fuskantar takkadamar ciniki, lamarin da ya haddasa karin hadura ga kasuwannin duniya, gami da matsin lamba ga tattalin arzikin Sin.

To, ta yaya za a iya daidaita wadannan matsaloli? Yayin da yake ziyara a lardin Guangdong, shugaba Xi Jinping ya ce, manufar yin gyare-gyare da bude kofa, muhimmiya ce ga tabbatar da makomar kasar Sin. Ya ce, "Cikin shekaru 40 da suka gabata, ci gaban da kasar Sin ta samu wajen raya kasa ya burge mutanen duniya. Tun da mun zabi wata hanya mai dacewa, to, me zai hana mu ci gaba da bin wannan hanya? Ko da yake ana fuskantar wasu matsaloli, za mu yi kokarin daidaita su yayin da muke ci gaba da kokarin bin wannan hanya." Saboda haka, shugaban ya nanata cewa, kasar Sin ba za ta daina gyare-gyarenta ba, kuma ba za ta dakatar da bude kofarta ba. Maimakon haka, za ta ci gaba da gudanar da manufar gyare-gyare da bude kofa don cimma wani sabon matsayi mafi inganci.

Sai dai, ta yaya za a samu cimma burin da shugaban ya saka? Idan muka dubi jawaban da shugaba Xi ya yi yayin da yake rangadi a lardin Guangdong, za mu san akwai a kalla fannoni 4 da za a lura da su.

Da farko, kasar Sin za ta kara kokarin kirkiro sabbin fasahohi. Kasar Sin ta gabatar da manufar raya kasa ta hanyar kirkiro sabbin fasahohi a shekarar 2012, sa'an nan a shekarar 2017, ta saka wani buri na zama daya daga cikin kasashe mafi mallakar fasahohi masu ci gaba zuwa shekarar 2035. Zuwa yanzu, mun ga wasu nasarorin da aka samu a wannan fanni, ga misali, kasar ta riga ta zama cikin jerin kasashe 20 mafi mallakar fasahohi da kungiyar kare ikon mallakar ilimi ta duniya ta gabatar a shekarar 2018, kana wata babbar gadar da ta hada Hongkong, Zhuhai da Macao na kasar Sin, wadda aka fara amfani da ita ba da dadewa ba, ta kunshi sabbin fasahohi fiye da 400, wadanda injiniyoyi Sinawa suka kirkiro.

Na biyu, za a kara kokarin zamanintar da masana'antun kasar Sin. Cikin shekaru 40 da suka wuce, kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannin raya masana'antu. A shekarar 2010, kasar ta riga ta zama kasar da ta fi samun karfin masana'antu a duniya. Sai dai har yanzu kayayyakin da ake samarwa a kasar ba kayayyaki masu daraja sosai ba ne. La'akari da wannan yanayin da ake ciki, shugaba Xi Jinping, yayin da yake rangadi a lardin Guangdong, ya bukaci a raya masana'antu masu fasahohin ci gaba.

Na uku, za a kara gina yankunan ciniki mai 'yanci don aiwatar da manufar bude kofa ta kasar Sin. Bayan shekarar 2012, sannu a hankali kasar Sin ta kafa yankunan ciniki cikin 'yanci na gwaji guda 12, wandada suka zama sabon dandalin ci gaba da aiwatar da manufar bude kofa ta kasar. Ban da haka, kasar na shirin kafa wani yanki na musamman dake dab da bakin teku wanda zai kunshi lardin Guangdong da yankunan Hongkong da Macao a ciki. Wannan yanki zai zama wata cibiyar hada-hadar kudi, da ta kirkiro sabbin fasahohi, wanda ke da tasiri a duniya.

Na hudu, kasar za ta yi kokarin tabbatar da samun daidaito a fannin ci gaban tattalin arzikinta. Za a dauki matakan bude kofa mafi inganci don tabbatar da ganin sassa daban daban na kasar dukkansu sun samu ci gaban iri daya. Yayin da yake rangadi a lardin Guangdong, shugaba Xi Jinping ya jaddada bukatar daidaita matsalar rashin daidaito wajen samun ci gaba tsakanin birane da kauyuka.

Yayin da ake murnar cika shekaru 40 da fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida, da bude kofa ga kasashen waje, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi amfani da rangadinsa a lardin Guangdong na kasar, don nuna ma mutanen duniya wani sako mai yakini, wato kasar Sin za ta ci gaba da gyare-gyarenta a gida, da kara bude kofa ga kasashen waje. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China