in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta yi nasarar kawar da ciwon shan inna
2018-10-25 10:05:40 cri

Sakamakon ci gaba da jajurcewa, hadin gwiwa da hada karfi da karfe, wajen yaki da ciwon shan inna wato polio a Najeriya, an samu gagarumar nasara, in ji wani babban jami'i.

Da yake jawabi a Abuja, babban birnin kasar, a lokacin bikin tunawa da zagayowar ranar yaki da cutar polio ta kasa da kasa ta shekarar 2018, Saadu Salahu, kakakin hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasar ya ce, ya zuwa watan nan na Oktoba, ba'a samu rahoton bullar cutar a fadin kasar ba sama da watanni 25 da suka gabata.

Ya ce, akwai rahotanni na cutar nau'in 2 wanda aka samu a matsayin samfurin, amma a cewarsa, wannan ba ainihin cutar polio da ake kokarin yakarta ba ne wadda ta nuna alamun kama da cutar ta polio.

A cewarsa, cutar ta nau'in 2, an same ta ne a sakamakon shafe shekaru masu yawa ana samun karancin zagayen alluran riga kafin da ya hade ko ina.

Ya ce, sakamakon hakan ya sa aka gudanar da cikakken gangamin yaki da barkewar cutar a zagaye na biyu wanda aka fara daga wata Mayu da Satumba zuwa Oktoban shekarar 2018, in ji kakakin.

Ya kara da cewa, gwamnatin Najeriya da hukumomin dake tallafawa yaki da cutar sun shirya gudanar da alluran rigakafin yaki da cutar a yankunan hukumomi 92 a fadin kasar daga watan Nuwamban shekarar 2018 domin kara baiwa al'ummar kasar kariya daga cutar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China