in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka Za Ta Lalata Tushen Zaman Lafiyar Duniya In Dai Ta Kare Aniyarta Ta Janye Jiki Daga Yarjejeniyar INF
2018-10-24 19:52:29 cri
A jiya Talata, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya gana da mai taimakawa shugaban kasar Amurka ta fannin harkokin tsaro John Robert Bolton, ganawar da aka gudanar bayan da shugaba Trump na Amurka, ya yi shelar janye jiki daga yarjejeniyar hana amfani da makami mai linzami na nukiliya mai cin gajere da matsakaicin zango wato INF a takaice.

Rahotanni na cewa, a yayin ganawar ta su, shugaba Putin ya yi suka game da yadda Amurka ta zargi Rashan da keta yarjejeniyar. Sai dai a nasa bangaren, Bolton ya ce, bai zo da nufin yin shawarwarin wanzar da zaman lafiya ba. Don haka, bangarorin biyu ba su cimma daidaito game da yarjejeniyar ba.

Tsohuwar tarayyar Soviet da Amurka sun daddale yarjejeniyar ne a ranar 8 ga watan Disamban shekarar 1987. Bisa ga yarjejeniyar, kasashen biyu za su daina mallakar makamai masu linzami dake cin zango tsakanin kilomita 500 zuwa 5500, ko kuma kerawa da gwajinsu. A watan Mayun shekarar 1991, an fara aiwatar da yarjejeniyar daga dukkan fannoni, a lokacin, tsohuwar tarayyar Soviet ta lalata makamai masu linzami kimanin 1752, a yayin da Amurka daga nata bangaren ta lalata 859. Don haka, ana daukar yarjejeniyar a matsayin yarjejeniyar kwance damara da ta fi gudana yadda ya kamata a lokacin yakin cacar baki.

To, amma me ya sa Amurka ke neman janye jiki daga yarjejeniyar? Hakan na da nasaba ne da manufar "mai da moriyar Amurka a gaban kome" ne.

Na farko dai, Amurka tana neman farfado da sojojinta, da kuma bunkasa makamai. A farkon lokacin da yake neman zabe, sai shugaba Trump ya gabatar da cewa, in dai ya ci zaben, zai yi kokarin bunkasa harkokin soja na kasar, ciki har da fasahohin zamani na kera makamai masu linzami.

Na biyu, kasar Amurka na fatan cimma burin karfafa masana'antun kera kayayyakin soja, ta hanyar wuce kayyadewar wasu yarjejeniyoyi. Masana'antun kera kayayyakin soja babbar sana'ar kire-kire ce. Tun bayan da Trump ya dare kujerar shugabancin kasar, ya dauki manufar farfado da masana'antun soja, ta hanyar amfani da yawan kasafin kudi don inganta masana'antun soja, da wuce kayyadewar kasar, da ma wanda duniya ke yi kan masana'antun sojan kasar. Ana iya cewa, kasar Amurka ta janye jiki daga yarjejeniyar INF ba domin dalilin siyasa kawai ba, har ma da nufin neman moriyar tattalin arziki.

Ban da wannan kuma, Trump ya zabi wannan lokaci don janye jiki daga yarjejeniyar INF, da nufin cimma burinsa a fannoni guda biyu: Da farko akwai yunkurin dauke hankalin al'ummar Amurka daga batun kisan dan jaridar nan dan asalin karsar Saudiyya Jamal Khashoggi, na biyu shi ne neman goyon baya daga wajen masu cinikayya a fannin makamai, da masu tsattsauran ra'ayi, da kuma masu ra'ayin rikau a zaben tsakiyar wa'adin majalisar dokokin kasar. A yayin da take tsaida kudurin janye jiki daga yarjejeniyar, ai bai manta ba ya shigar da kasar Sin cikin batun, da nufin karfafa abubuwan fifiko a yayin da yake shawarwari da Rasha. A sa'i guda kuma yana son kara mai da kasar Sin a matsayin wadda ta tayar da takkadamar, ta yadda zai iya samun goyon baya daga wajen masu jefa kuri'u mafiya yawa a zaben.

A hakika dai, yarjejeniyar INF wata yarjejeniyar bangarori biyu ce a tsakanin Amurka da Tsuhuwar tarayyar Soviet. Ba ta da kuma alaka da kasar Sin, kuma kasar Sin mamba ce ta sa hannu kan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, amma Amurka na ci gaba da karya martabar yarjejeniyar kwance damarar makaman kare dangi a idanun kasashen duniya, hakan zai kawo illa ga dukkan tsarin hana yaduwar makaman nukiliya da kayyade damara na kasa da kasa, tare kuma da kawo hargitsi ga zaman lafiyar duniya.

A cikin dogon lokaci na tsawon shekaru daruruka da aka bunkasa alaka a tsakanin kasa da kasa, aka kafa wani tsari a tsakanin kasashe masu mulkin kai, wato sun sanya hannu kan yarjejeniyoyi daban daban, don ba da tabbaci ga gudanar da harkokin kasa da kasa yadda ya kamata. Amma, jerin matakan da Trump ya dauka na janye jiki daga yarjejeniyoyi da kungiyoyi ko hukumomi sun girgiza da wannan tushe, kuma ba su amfana wajen bin sabbin yarjejeniyoyin da za a cimma a tsakanin kasa da kasa a nan gaba ba.(Masu fassara: Lubabatu Lei, Bilkisu Xin, ma'aikatan sashen Hausa na CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China