in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban rukunin Roche: CIIE da za a kaddamar a Sin zai sa kaimi kan cinikin kasa da kasa
2018-10-23 15:57:41 cri

Za a kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa dasu daga ketare na kasa da kasa a birnin Shanghai na kasar Sin wato CIIE a takaice, wasu manyan kamfanoni a fadin duniya suna share fage domin halartar wannan gagarumin biki. Kwanan baya yayin da shugaban majalisar mashawarta ta rukunin hada magani na F. Hoffmann-La Roche na kasar Swiss Christoph Franz yake zantawa da manema labarai, ya bayyana cewa, bikin CIIE zai sa kaimi kan cinikayyar kasa da kasa.

Christoph Franz ya bayyana cewa, rukuninsa yana maida hankali matuka kan bikin CIIE, dakin baje kolin kayayyakinsa da aka kebe a cibiyar baje kolin Shanghai yana da girma sosai, shi kansa zai halarci bikin.

Rukunin Roche, rukunin hada magani ne da ya kai sahun gaba a fadin duniya, har ya kai matsayi na 169 daga cikin manyan kamfanoni mafiya girma a fadin duniya a shekarar 2018, shugaba Franz ya ce, duk da cewa, a halin da ake ciki yanzu wasu kasashe suna bada kariya ga cinikayyar cikin gida na kasashensu, amma manyan kamfanonin da yawansu ya kai 2800 da suka zo daga kasashen duniya daban daban zasu taru wuri guda yayin bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa dasu daga ketare da kasar Sin ta karbi bakuncin shiryawa, hakan ya nuna cewa, bikin CIIE ya jawo hankalinsu matuka, a cewarsa: "A wasu kasashe, ana kara bada kariya ga cinikayyarsu, a karkashin irin wannan yanayi, ya zama dole a kara karfafa muhimmnacin gudanar da cinikayyar dake tsakanin kasa da kasa saboda zata ciyar da tattalin arzikin duniya gaba, yanzu haka kasar Sin tana kokarin shirya bikin CIIE karo na farko, ko shakka babu lamarin zai sa kaimi kan cinikayyar kasa da kasa, kana a bayyane an lura cewa, ya kasance huldar moriyar juna dake tsakanin kasar Sin da abokan cinikayyarta."

Shugaba Franz ya yi mana bayani cewa, rukuninsa zai baje kolin sabbin magungunan sha wanda ya hada a yayin bikin, misali rukunin ya hada wani sabon nau'in maganin ciwon dajin huhu bada dadewa ba, a don haka karo na farko ne zai nuna maganin ga kasa da kasa a yayin bikin Shanghai, kana yawan ma'aikatan rukuninsa dake aiki a Shanghai wadanda zasu halarci bikin zai kai sama da dari daya, yana mai cewa, "Makasudin da muka yi haka shine domin nunawa kasa da kasa cewa, rukuninmu yana mayar da kasar Sin, musamman ma birnin Shanghai na kasar a matsayin babbar cibiyar reshenmu a fadin duniya, mun hakikance cewa, bikin CIIE karo na farko da za a kaddamar a Shanghai zai sa kaimi kan ci gaban tsarin kirkire-kirkire a fadin duniya, rukunin Roche shi ma yana sa ran zai shiga tsarin."

Shugaba Franz ya kara da cewa, yanzu rukuninsa yana gudanar da aikinsa a kasashe 100 a fadin duniya, amma ya kafa cibiyar hada magani da cibiyar nazarin fasahar hada magani a kasashe 5 ne kawai, kasar Sin tana cikinsu, hakan ya nuna cewa, rukunin yana maida hankali matuka kan kasar Sin, Franz ya ci gaba da cewa, yana fatan zai kara karfafa cudanyar dake tsakanin rukuninsa da kasar Sin, dalilin da yasa haka shine domin ba ma kawai yana mayar da kasar Sin babbar kasuwarsa kawai bane, har ma yana mayar da babbar cibiyar kirkire-kirkirensa a fadin duniya, ya ce, "Yanzu kwararrun masana kimiyya da fasaha suna karuwa cikin sauri a kasar Sin, a don haka muna fatan zamu iya kara karfafa huldar dake tsakaninmu da kasar Sin, kana rukunin Roche ya kafa cibiyar nazarin fasahar hada magani a birnin Shanghai, ina ganin cewa, cibiyar da aka kafa a Shanghai zata kawo tasiri ga ci gaban aikin hada maganin kasar Sin."

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, kasar Sin tana gudanar da kwaskwarima kan tattalin arzikinta, hakan yasa kasar ta Sin ta gamu da matsaloli a fannoni da dama, ban da haka, saurin karuwar tattalin arzikin kasar shima ya saukaka, wato daga karuwa cikin sauri zuwa karuwa bisa matsakaicin yanayi, Franz ya bayyana cewa, tun bayan da rukuninsa ya shiga kasar Sin a shekarar 1926, har kullum yana cike da imani kan makomar kasar Sin, a cikin shekaru biyar da suka gabata, gaba daya adadin jarin da rukunin ya zuba a kasar Sin ya kai kudin Sin RMB biliyan 8 da miliyan 400, yana mai cewa, "Rukunin Roche yana cike da imani kan makomar kasar Sin, ana iya gano wannan daga aikin da ya gudanar a kasar a tsawon shekaru sama da 90, duk da cewa, mun taba gamuwa da wasu wahalhalu, amma muna yin kokarin kawar da wahalhalun tare da al'ummun kasar Sin a koda yaushe."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China