Dandalin inganta cinikayya da ci gaba na MDD UNCTAD ne ke shirya taron na manyan jami'ai da kan gudana bayan shekaru 2, domin magance batutuwan da suka shafi zuba jari.
Sakatare Janar na dandalin UNCTAD Mukhisa Kituyi, wanda ya ce tattalin arzikin duniya na cikin yanayi na rashin tabbas fiye da shekaru 10 da suka wuce, ya ce taron da zai gudana daga ranar 22 zuwa 26 ga wata, ya samu mahalarta 6,000, ciki har da shugabannin kasashen 12 da kuma shugabannin kamfanoni masu zaman kansu sama da 50.
Ya kara da cewa, suna neman yadda za a magance kalubalen da ake fuskanta da lalabu manufofi, ta yadda za a mayar da hankali da hadin kai tsakanin shugabanni, kan damamakin dake tattare da tattalin arzikin duniya maimakon matsalolin da yake da su.
Ya ce shawo kan wadancan kalubale na da muhimmanci ga ci gaban duniya a hanyoyin cimma muradun ci gaba masu dorewa na MDD ya zuwa shekarar 2030.
Mukhisa Kituyi ya ce taron zai taimaka wajen tsara manufoofin da za su taimaka wajen sauya manufofin zuba jari na duniya, ta yadda za su dore. (Fa'iza Mustapha)