in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya bayyana hanyar da kasarsa za ta bi
2018-10-22 11:19:36 cri

A tarihin bil Adama, har kullum shahararrun 'yan siyasa da masu zurfin tunani sun kware wajen gabatar da bayyanai masu kunshe da shawarwari, shugabannin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin su ma haka suke, misali shugaban kolin kasar Sin Xi Jinping ya kware matuka a wannan fannin.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kware matuka wajen yada manufofin kasa ta hanyar bayyana labarai masu ban sha'awa, misali a yayin da yake gabatar da jawabai a wuraren taruka ko kuma yayin da yake gudanar da rangadin aiki a wurare daban daban a fadin kasar, ko a lokacin da yake gabatar da jawabai a kasashen ketare, ko kuma yayin da yake rubuta rahoto a jarida ko mujalla, har kullum ya fi son nuna ra'ayi mai babbar ma'ana ta hanyar gabatar da kananan labarai masu ban sha'awa, an lura cewa, hakan yana iya jawo hankalin masu sauraro cikin sauki, kuma yakan nunawa masu sauraro hikima da karfi na Sinawa, a sa'i daya kuma, ana iya gano cewa, shugaba Xi yana da ilmomi masu yawa. To, tun daga yau bari mu gabatar muku shirye-shirye a jere kan wannan wato labarai da Xi Jinping ke gabatarwa, ga labari na yau mai taken "hanyar da kasar Sin za ta bi".

Tun bayan da aka fara aiwatar da manufar yin kwaskwarima kan tattalin arzikin kasar Sin da bude kofa ga kasashen waje, cikin sauri hadadden karfin kasar yana kara karuwa, haka kuma karfin kawo tasiri a fadin kasashen duniya yana karuwa a kai a kai, a don haka al'ummomin kasashen duniya suna kara mai da hankali kan kasar ta Sin, amma yayin da suke nuna yabo da fahimta, suma sun bayyana shakku da damuwa gareta.

A watan Oktoban shekarar 2015, shugaba Xi ya taba kai ziyara a kasar Birtaniya, ya kuma taba gabatar da wani jawabi a cibiyar harkokin kudi ta birnin Landan, domin nunawa kasa da kasa manufofin da kasarsa ke aiwatarwa yayin da take kokarin raya ci gaban kasa daga dukkan fannoni, inda ya bayyana cewa, "Sinawa suna kan hanyar da suka zaba bisa hakikanin yanayin tarihin da kasar Sin ke ciki, an ce, hanyar da ake bi zata kawo makomarsu a nan gaba, muddin dai wata kasa ko wata kabila ta zabi hanyar da tafi dacewa, to zata cimma burin samun ci gaba, tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyaran fuska da bude kofa ga kasashen waje a cikin shekaru 37 da suka gabata, adadin karuwar tattalin arzikin kasar ya kai kaso 10 bisa dari a ko ace shekara, har ta kasance kasa ta biyu wajen saurin ci gaban tattalin arziki a fadin duniya, abu mai faranta ran mutane shine, al'ummun kasar da yawansu ya kai sama da miliyan 600 sun kubuta daga kangin talauci, haka kuma kwatankwacin GDP na kowace al'ummun kasar ya kai dalar Amurka dubu 7. A bayyane take abin lura a nan shine, kasar Sin ta samu sakamakon ne cikin shekaru sama da goma kawai, amma sauran kasashen da suka ci gaba sun shafe shekaru sama da daruruwa, duk wadannan sun shaida cewa, Sinawa suna kan hanyar data fi dacewa yayin da suke kokarin samun ci gaba."

Kafin kafuwar sabuwar kasar Sin a shekarar 1949, kasar ta taba gamuwa da matsaloli masu tsanani da dama, shugaba Xi ya ambata sunan marigayi Sun Yatpsen wanda ya taba jagorancin juyin juya halin demokuradiyar kasar Sin, shi ma ya bayyana cewa, Sinawa sun taba shan wahalhalu masu tsanani da dama kafin suka zabi hanyar da suke bi wato hanyar gurguzu, yana mai cewa, "Sinawa sun zabi hanyar gurguzu ne bisa hakikanin yanayin tarihin da suke ciki, kamar yadda mai zurfin tunani na Birtaniya Bertrand Russell ya bayyana, 'Sinawa sun fi gane kansu, Sinawa su da kansu ne kawai zasu iya samun hanyar ci gaba mafi dacewa.' Hakika har kullum Sinawa suna maida hankali kan kwaskwarima da kirkire-kirkire, mun zabi hanyar gurguzu ne domin mun lura cewa, ta fi dacewa da yanayin da kasarmu ke ciki, yanzu haka mun ciyar da tsarin gurguzu gaba har ya kasance tsarin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin, wato muna kokarin gina tattalin arzikin kasuwar gurguzu, da siyasar demomuradiya, da al'adu masu ci gaba, da zamantakewar al'ummar zaman jituwa, da wayewar kan hallitu masu rai da marasa rai, tare kuma da sa kaimi kan ci gaban bil Adama da adalci, ta yadda za a cimma burin samar da wadata ga daukacin al'ummun kasar baki daya. Babu wata hanyar da zata dace da kowace kasa, muddin dai aka zabi hanyar zata samar da moriya ga al'ummun kasar, sai dai ana iya cewa, hanyar tana cike da kuzari, har zata ciyar da kasar gaba yadda ya kamata"(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China