A lokacin zantawar tasu ta wayar tarho, sun cimma matsaya cewa duk wanda aka samu da hannu a mutuwar dan jaridar wajibi ne a gurfanar da shi a gaban shara'a, kakakin shugaban kasar Turkiyya ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.
Erdogan tun da farko ya fada a ranar Lahadi cewa, zai yi cikakken bayani game da batun mutuwar Khashoggi a ranar Talata a lokacin da zai gana da 'yan jam'iyyarsa a majalisar dokoki.
Marigayi Khashoggi, dan jaridar kasar Saudiyya ne, an dena jin duriyarsa tun bayan da ya shiga karamin ofishin jakadancin Saudiyya dake birnin Istanbul a ranar 2 ga watan Oktoba.
A ranar Asabar da ta gabata masarautar Saudiyya ta sanar da cewa Khashoggi ya mutu ne a sanadiyyar barkewar fada a karamin ofishin jakadancinta, amma ba ta yi cikakken bayani kan masabbabin mutuwar dan jaridar ba. (Ahmad Fagam)